‘Bala mai son wasa’
Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai son wasa’. Labarin ya yi nuni ne ga illar da yawan wasa ke janyo wa mutum. A sha karatu lafiya. Taku; Amina Abdullahi. Bala yaro ne wanda yake son yin wasanni da dama gashi kuma iyayensa […]
Assalamu alaikum Manyan gobe tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Bala mai son wasa’. Labarin ya yi nuni ne ga illar da yawan wasa ke janyo wa mutum. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
Bala yaro ne wanda yake son yin wasanni da dama gashi kuma iyayensa sun kasance talakawa ne. Mahaifinsa yana iya bakin kokarinsa domin ganin dansa ya samu ilimi mai inganci a wannan garin. Idan malamin Bala yana koyar da su a aji Bala hankalinsa na waje. Walau yana kallon su kadangaru ko kuma tumakai masu wucewa. Hakan ya sa ya dauki ya zama na kashin baya a ajinsu.
Saboda wasa, ko aikesna aka yi sai ya zubar da kudin sannan ya koma gida. Mahaifiyarsa abin ya dame ta don haka take jibgarsa a duk lokacin da ta aike shi kuma ya zubar mata da kudi.
Bala yakasance yaro dan shekara 10. Ran nan sai mahaifiyar ta ga ya yi fitsarin kwance. Koda ta tambaye shi dalilin yin hakan sai ya ce mata ya yi mafarki ne suna tsakiyar wasa sai ya yi fitsari. Da mahaifinsa ya samu wannan labari shi ma sai ya shiga jibgarsa.
Tare da fatan Manyan gobe za su dauki darasi game da wannan labarin. Yawan wasa na sanya Manyan gobe yin munanan halayya. Sai a rage.