Bala Mohammed ya kafa kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya kafa kwamitin binciken zaluncin jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar. Gwamna Bala ya kafa kwamitin ne a ranar Laraba domin bincikar laifukan ‘yan sanda a jihar biyo bayan korafe-korafe da jama’ar jihar suka shigar gaban gwamnatin jihar, bisa laifukan da suka shafi zalunci da cin zarafin al’umma. Lalong […]

Bala Mohammed ya kafa kwamitin binciken zaluncin ‘yan sanda

Gwamnan Jihar Bauchi Bala Mohammed

Gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed, ya kafa kwamitin binciken zaluncin jami’an ‘yan sanda na SARS a jihar.

Gwamna Bala ya kafa kwamitin ne a ranar Laraba domin bincikar laifukan ‘yan sanda a jihar biyo bayan korafe-korafe da jama’ar jihar suka shigar gaban gwamnatin jihar, bisa laifukan da suka shafi zalunci da cin zarafin al’umma.

Gwamnan ya bawa kwamitin tsawon watanni shida ya gudanar da binciken tare da gabatar masa da sakamako domin daukar matakin shari’a da ya dace.

Kwamitin karkashin jagorancin tsohon Mai Shari’a Habibu idris a matsayin shugaba, sai tsohon Shubagan Hukumar ‘Yan Sandan jihar CP Hamisu Makama da kuma sauran masu ruwa da tsaki a jihar daga kungiyoyi masu zaman kansu a matsayin mambobi.

Ana sa ran kwamitin zai fara gudanar da aikinsa daga mako mai zuwa domin samar da sakamakon bincikensa a kan lokaci.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa