Bala Mohammed ya zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

Bala Mohammed ya maye gurbin Gwamnan Oyo, Seyi Makinde

Bala Mohammed ya zama Shugaban Kungiyar Gwamnonin PDP

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Muhammad ya zama shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar PDP ta Kasa.

Bala ya samu nasarar dare kujerar ne a wani taro da gwamnonin PDP suka gudanar a Jihar Bauchi wanda ya samu halarcin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar.

Da yake jawabi, gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya ce sun cimma matsayar ne bisa lura da cewa Bala Muhammad zai iya jagorantar kungiyar yadda ya kamata.

Kazalika, ya sanar da cewa gwamnonin PDP din sun kuma zabi gwamnan Jihar Ribas, Siminalayi Fubara a matsayin mataimakin shugaban kungiyar.

Bayanai sun ce an gudanar da zaben ne a dakin taro da ke Fadar Gwamnatin Bauchi.

Bala Mohammed ya maye gurbin Gwamnan Oyo, Seyi Makinde wanda shi ma ya halarci taron na yini guda da aka gudanar a wannan Asabar din.

Tsohon Kwamishinan Kano ya sauya sheƙa daga NNPP zuwa APC

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’