Balahirar Fyade: Jan hankali ga iyayen yara da al’umma (1)
Babban Lauya, Ustaz yusuf O. Ali (SAN) ya gabatar da wannan mukala a taron Makon Lauyoyi.
Babban Lauya, Ustaz yusuf O. Ali (SAN) ne ya gabatar da wannan mukala a taron Makon Lauyoyi Mata da Kungiyar Lauyoyi Mata ta Kasa (FIDA) reshen Jihar Ekiti ta shirya a 2017.
Muhimmancin mukalar da dacewarta da wannan lokaci ya sa Barista M. B. Mahmoud Gama ya fassara:
Gabatarwa:
Da farko dai ina mika godiyata ga wadanda suka shirya wannan taro saboda jajircewarsu wajen ganin wannan taro ya tabbata.
Sannan ina gode musu matuka saboda zabe na da suka yi don gabatar da wannan mukala a wannan taro mai albarka kuma mai tarihi.
Ina kuma yaba musu matuka saboda hangen nesan da suka yi wajen zabar wannan maudu’i a irin wannan lokaci da fyade ga kananan yara ya zama ruwan dare a cikin al’ummarmu.
Babu shakka, yara ababen tattali ne ga kowace al’umma saboda amannar da aka yi da cewa su ne Manyan Gobe.
To amma duk da wannan tagomashi da matsayi mai girma da yaran ke da su a idon al’umma, wannan bai hana wasu bata-gari, marasa imani, a wasu lokutan, cin zarafin yaran ba ta fuskoki iri daban-daban; ciki har da aikata musu wannan babban cin zarafi na yi musu fyade, don kawai raunin hankali da zubin halittarsu da karfin jiki da rashin iya tsinkayar abin da ka-je-ya-zo da su yaran ke da shi.
To amma ni a nan, zan mayar da hankali ne wajen bayanin cin zarafin yaran ta fuska daya ne, wato fyade, sannan mu duba mu gani, wace irin rawa iyaye da al’umma da sauran wadanda Allah Ya dora wa hakkin kula da yaran ke takawa wajen ba da kofa ko akasin haka wajen aikata wannan ta’annati.
Wane ne yaro kuma mene ne fyade?
Yaro:
A karkashin Sashi na 277 na Kundin Dokokin ’Yancin Yara (Child Rights Act) 2003, ta fayyace yaro da cewa, “shi ne mutumin da bai kai shekara 18 ba.”
Haka ita ma Dokar Masu Aikata Laifuffuka ta Intanet, Cyber Crime (Prohibition, Prevention, Etc) 2015 ta fassara.
Dokokin Majalisar Dinkin Duniya sun fassara “Yaro” da cewa shi ne, “duk dan Adam din da yake kasa da shekara 18, sai fa in kasar da yaron yake ce a dokokinta, ta rage zuwa kasa da shekara 18 din.”
Abin da za mu iya hasasowa daga sassan wadannan dokoki da muka zayyano shi ne, lallai “Yaro,” dangane da karancin shekaru da dokokin suka nuna, yana bukatar kulawa da ba shi kariya daga dukkan wani abu da zai cutar da shi ko razana shi a rayuwarsa.
Fyade:
Fyade dai, a dunkule shi ne yin jima’i ba tare da yardar daya daga cikin masu yin jima’in ba amma duk da haka, aka tilasta wa dayan har aka samu fakuwar azzakari a cikin farji a tsakaninsu, an samu maimaituwar hakan a kai-a kai ko ba a samu ba. Niyyar aikata fyaden ba ya zama aikata fyaden.
A kundayen laifuffuka daban-daban da ake da su, ma’anar na canzawa daga wannan kundi zuwa wancan.
Ma’ana, babu wata tartibiyar fassara da aka yi ittifaki a kanta.
Ga misali, kungiyar nan ta Afrika mai suna African Network for the Prevention and Protection Against Child Abuse and Neglect (ANPPCAN) ta fayyace yin fyade ga kananan yara da cewa, “wani yanayi ne da akan jefa yaro ko yarinya ’yan kasa da shekara 18 cikin yi jima’i ba tare da amincewarsu ko rashin amincewarsu ba.”
A nan, yarda ko rashinta ba abin la’akari ba ne.
Kungiyar ta ci gaba da cewa, kuma shaidar an yi jima’i da yaro ko yarinyar shi ne, lallai a ga alamar an samu fakuwar azzakari a cikin farjin yarinyar ta hanyar samun bayanin likita wajen tabbatar da cewa, an ga jini ko maniyyi ko kujewa a jikin farjin ko duburar.
A nan, abin da kungiyar ta ANPPCAN ke tabbatarwa shi ne, dole a samu fakuwar azzakari cikin farji kafin a ce an yi fyade.
Ita kuwa Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO), na ganin yin fyade ga karamin yaro ko yarinya a matsayin “jefa su cikin yin jima’in da kwata-kwata ba su san mana’ar yinsa ba; ko saboda ba su kai matsayin yi ba, balantana su nuna amincewarsu. Ko kuma sun yarda da yin jima’in don gudun saba wa wata al’adar.”
Saboda haka, yin fyade a wajen WHO, yana samuwa ne tsakanin babban mutum da kuma karamin yaro kawai.
Marubuta, Lorain da Andrew, a kokarinsu na fito da ma’anar fyade ga kananan yara, a wani bincike da suka yi a Kudancin Afrika, sun kalailaice ma’anar fyade ga kananan yara.
Su a wajensu, yin fyade ga kananan yara iri biyu ne da ya kamata a lura da su kuma a fahimce su.
Na farko shi ne, fyaden da aka yi shi ta hanyar saduwa kai-tsaye, wanda ya hada da taba al’aurar yaro ko yarinya; ko a sa yaron ko yarinyar su taba, ko yin wasa da al’aurar wani; ko kuma a’a, a sanya wani abu ko wata gaba (kamar yatsa ko harshe ko kuma azzakari) a cikin farjin yarinya ko bakinta, duk don neman jin dadi, ko don samun gamsuwa irin ta jima’i.
Sai na biyu, shi ne wanda ba a samun saduwa ta kai-tsaye. Misalinsa shi ne, nuna wa yara bidiyon batsa ko mutum ya dinga nuna musu al’aurarsa da gangan ko nuna musu hotunan batsa, da sauransu.
Ya kamata kuma a sani, a karkashin dokokin Najeriya, mutum zai tabbata ya yi wa karamar yarinya fyade ne kawai, ba tare da yin la’akari da yardarta ya yi ko ba da yardarta ba.
Abin nema kawai, wadancan abubuwan da muka ambata a sama su tabbata.
Dalili kuwa shi ne, kunshiyar Dokokin ’Yancin Yara cewa ya yi, ba a yarda wani mutum ya yi jima’i da karamar yarinya ba – da yardarta ko ba da yardarta ba, wanda hukuncin aikata hakan zai iya jaza wa mutum zaman gidan yari na rai-da-rai!
Kunshiyar dokar ba ta ba da damar fakewa da rashin sanin shekarun yarinyar ba (kamar mutum ya ce ai ban san ba ta kai shekara 18 ba; ko kuma ya ce ai na dauka ta kai shekara 18, shi ya sa na yi jima’i da ita).
Haka ma dokar, ba ta ba da kofar mutum ya ce, ai na nemi izininta ko yardarta kafin in yi jima’i da ita.
Duk wadannan uzirori ne da ba su da nauyi a idon shari’a.
Domin kuwa ba yadda za a yi yarinya ’yar shekara 11 zuwa kasa ta san ma’anar yarda ko rashin yarda wajen yin jima’i da ita!
Saboda haka in a kotu ce, za ta tafi a kan cewa ba da yardarta ba aka yi jima’i da ita, ko da kuwa da yardarta ce tun farko.
Saboda a idon shari’a, yarinya karama ba ta cikin jerin wadanda doka ta amince a yi jima’i da su, don me kuwa za a nemi yardarta tun farko? Wannan ita ce matsayar shari’a.
Za mu ci gaba