Bala’in da matan da ’yan Bindiga suka koro ke ciki a Neja

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Jihar Neja ta Arewa sun ce matan da aka karkashe mazansu da kuma ’yan matan da aka kashe musu iyaye daga ƙauyuka sama da 80  a Karamar Hukumar Mariga ta kihar suna rayuwa ne a cikin bala’i. Kungiyar ta ce matan suna rayuwa cikin wahalhalu daban-daban ba tare da samun tallafi daga […]

Bala’in da matan da ’yan Bindiga suka koro ke ciki a Neja

Irin barnar da ’yan bindiga suka yi a kauyen Matane, Jihar Neja. (Hoto: Abubaka Akote).

Gamayyar Kungiyoyin Matasan Jihar Neja ta Arewa sun ce matan da aka karkashe mazansu da kuma ’yan matan da aka kashe musu iyaye daga ƙauyuka sama da 80  a Karamar Hukumar Mariga ta kihar suna rayuwa ne a cikin bala’i.

Kungiyar ta ce matan suna rayuwa cikin wahalhalu daban-daban ba tare da samun tallafi daga gwamnati ba duk kuwa da cewa yawancinsu suna cikin  rashin tabbas da barazanar fadawa halaka ta zinace-zinace da shaye-shayen miyagun kwayoyi domin neman abinci.

Matasan sun bayyana cewa, duk da yadda matan ke sha’awar kasuwanci da wasu sana’o’in dogaro da kai, rashin jari da wadataccen tallafin gwamnati na maida hannun agogo baya.

Sun kara da cewa wahalar ta kai ga wasu daga cikin zawarawa da ’yan matan da suka rasa mazaje da iyayensu yin karuwanci, yayin da wasu kuma ’yan bindigar suna tsare da su ba tare da an iya ceto su ba.

A wani taron manema labarai da suka gudanar a Minna, shugaban kungiyar, Sahabi Mamuda Auna da sakatarensa Jibrin Aliyu Matane sun ce wasu matan kuma na yin auren je ka na yi ka domin kauce wa wahala.

Sun yi kira ga ministar harkokin mata ta Najeriya da ta taimaka wa zawarawa da ’yan mata a maimakon hana su aure da ta nemi yi, wanda suka kira da yunƙurin shiga sha’anin addini.

Kungiyar ta ce Karamar Hukumar Mariga, na daga cikin wuraren da ta’addancin ’yan bindiga ya fi kamari, inda ya yi sanadiyar tashin  sama da ƙauyuka 80.

Sun ce, wannan bala’i ya tilasta wa ’yan ƙauyukan yin watsi da gidajensu da kadarorinsu da sana’o’insu, domin neman tsira.

Hakazalika sun ce da yawa daga cikin masu dan abin yi yanzu sun koma bara da sauran munanan halaye a tsakanin al’umma.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja