Balaraben Qatar ya janye tayin sayen Manchester United
United tana mataki na 10 a teburin Premier League da maki 12.
Attajirin Balaraben nan dan kasar Qatar, Sheikh Jassim bin Hamad Al Thani, ya janye tayin da ya gabatar a kokarin sayen kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
BBC Sport ya ruwaito cewa, Sheikh Jassim ya yi tayin sayen United kan fam biliyan biyar, amma an katse cinikin a karshen makon da muka yi bankwana da shi.
- Gwamnati ta bai wa Direbobin Danfo wa’adin daina kasuwanci a kan gadojin Legas
- Kasashen Larabawa sun bukaci sojojin Isra’ila su fice daga Gaza
Iyalan Glazer, wadanda suka sayi kungiyar Old Trafford a 2005 kan fam miliyan 790, sun sanar a watan Nuwambar 2022 cewar suna tunanin sayar da kungiyar.
Wani dan attajirin dan kasuwa a Ingila, Sir Ratcliff mai rukunin kamfanin Ineos ya taya kungiyar, amma hannun jarin yake bukatar saya ba duka kungiyar ba.
Wani bincike da aka gudanar a watan Maris ya nuna ana bin United bashin fam miliyan 969, wadda ta lashe Carabao Cup a bara da samu gurbin Champions League.
A farkon watan nan, BBC ta bayar da rahoton cewar Ratcliff na duba yiwuwar sayen hannun jarin marasa rinjaye, ko zai rage karfin mamallakan kungiyar.
A bara iyalan Glazer sun sanar cewar suna duba yiwuwar sayar da United, wadda mutane da dama ke yin zawarci, sai dai Ineos da Sheikh Jassim suka yi tayi.
Kowannensu ya yi tayin biyan fam biliyan biyar, ciki har da attajirin duniya Elon Musk, abinda ya haifar da muhawara a tsakanin magoya baya da masu sharhi kan wasanni, amma daga bisani ya ce da wasa ya ke.
Sheikh Jassim ya fayyace cewar kungiyar yake son saya baki daya, shi kuwa Ratcliff hannun jari mafi tsoka yake bukatar saya.
Magoya bayan United sun sha yin zanga-zanga a ciki da wajen Old Trafford cewar ba sa bukatar iyalan Glazer a kungiyar.
United tana mataki na 10 a teburin Premier League da maki 12, bayan buga wasa takwas da fara kakar nan.