Balarabiya ta gaji Naira biliyan uku da miliyan 350 bayan mutuwar mijinta wata guda da aurensu
Wata bakuwar Balarabiya da ta auri dan Saudiyya ta gaji Riyal miliyan 67, wato daidai da Naira biliyan uku da miliyan 350 bayan wata guda da rasuwar mijintaHamshakin attajirin ya auri wannan mata ’yar shekara 22 ba tare da sanar da iyalanhsa ba. Sai wani dan uwansa da amininsa sun shaida yadda bikin auren ya […]
Wata bakuwar Balarabiya da ta auri dan Saudiyya ta gaji Riyal miliyan 67, wato daidai da Naira biliyan uku da miliyan 350 bayan wata guda da rasuwar mijinta
Hamshakin attajirin ya auri wannan mata ’yar shekara 22 ba tare da sanar da iyalanhsa ba. Sai wani dan uwansa da amininsa sun shaida yadda bikin auren ya gudana.
Daga bisani ya mutu bayan wata guda da wannan aure, inda ya yi fama da ciwon zuciya. Mutumin ya rasu ne a gidan amaryarsa, kamar yadda jaridar Al Marsad da ake wallafa a shafin intanet ta ruwaito. Iyalan marigayin sun yi yunkurin kin amincewa da amaryarsa, inda suka jajirce kan cewa, ‘ba su da masaniya, al’amarin da ya tursasa amaryar ta kai kara, har aka ba ta rabon tan a gado.
A birnin Jedda,. Lauyan da ya tsaya mata a kotu, ya fito da shaidar aure da kotu ta bai wa ma’auratan, sannan ya kiorawo dan uwan mamacin da amininsa suka bayar da shaida. Bisa wadannan hujjoji da aka gabatar wa kotu, sai ta yanke hukunci cewa, wannan amarya a bata rabonta na gadon mamacin. Jaridar Al-Marshada dai ba ta bayyana shekarun attajirin ba, sannan bat a bayyana kasar da amaryar ta fito ba.