balencia ta fara yunkurin dauke bictor baldes daga Manchester United
Da alama kulob din Manchester United da ke Ingila zai shiga rudu idan ya kuskura ya bar kulob din balencia na Sifen ya saye golansu na biyu bictor baldes. Tun cikin watan Janairun wannan shekara da bictor baldes ya koma kulob din Mancehster United bai buga wasan kirki ga kulob din ba, al’amarin da ya […]
Da alama kulob din Manchester United da ke Ingila zai shiga rudu idan ya kuskura ya bar kulob din balencia na Sifen ya saye golansu na biyu bictor baldes.
Tun cikin watan Janairun wannan shekara da bictor baldes ya koma kulob din Mancehster United bai buga wasan kirki ga kulob din ba, al’amarin da ya sa ya fara tunanin barin kulob din.
Kulob din balencia ya yi yunkurin saye golan Mardid Iker Casillas ne amma kulob din ya yi kememe da hakan ta sa ya karkata akalarsa ga kulob din United a kan baldes.
Wata jarida mai suna Super Deporte da ake wallafata a Sifen ta kalato kulob din balencia yana so ya yi wa baldes shigar sauri ne wajen saye shi kafin a fara kakar wasa mai zuwa. Idan hakan ta kasance akwai yiwuwar Manchester United ta raba gari da gololinta biyu watau Dabid De Gea da ake tunanin zai koma Real Madrid na Sifen da kuma bictor baldes da kulob din balencia ke yunkurin dauke shi.
Sai dai alamu sun nuna kulob din United yana yunkurin saye golan Chelsea Petr Cech kafin a fara kakar wasa mai zuwa.