Ballon d’Or: Ko Benzema zai lashe kambun bana?
Benzema ya kafa tarinin wanda ya fi shekaru da ya zura kwallo uku rigis a Gasar Zakarun Turai.
A ranar Litinin, 17 ga Oktoban bana ce za a yi bikin karrama gwarazan ’yan wasan kwallon kafa na duniya wato Ballon d’Or wanda Hukumar Kwallon Kafa ta Faransa ke shiryawa duk shekara.
Dan wasan Kungiyar PSG, Lionel Messi ne ya lashe kambun na bara, bayan ya doke dan wasan Kungiyar Barcelona a yanzu, Robert Lewandoski, wanda mutane da dama suka yi tsammanin zai lashe.
- Sadakin Naira dubu 50 tozarta aure ne —Sheikh Kaura
- ’Yan Najeriya 56 sun mutu sun bar dukiya babu magada a Birtaniya
Da lashe kambun na bara ne Messi ya zama ya lashe sau bakwai, wanda ba a taba samu a tarihi ba, sai Cristiano Ronaldo da ke biye masa da biyar.
Sai dai abin mamaki babu sunan Messi a jerin ’yan wasan da za a ba kyautar ta bana, wanda hakan ba ya rasa nasaba da rashin katabus da ya yi a kakar farko da ya je Kungiyar PSG.
Sai dai masu kallon kwallon kafa, musamman magoya bayan Kungiyar Real Madrid suna fata wannan karo Karim Benzema, dan wasan gaban Madrid ya lashe kambun lura da rawar da ya taka a kakar bara.
Duk da cewa kakar bara ake dubawa wajen bayar da kambun, a kakar bana ma dan wasan ya fara da kafar dama, inda shi ne ya zura kwallo ta biyu a wasan a minti na 65 da fara wasan da Real Madrid ta doke Kungiyar Frankfurt da ci 2-0.
Da wannan kwallo da ya zura ya kere tsohon kyaftin din kungiyar, Raul a jefe kwallaye, inda yanzu yake da kwallo 324 domin zama dan wasa na biyu da ya fi jefa kwallo a kungiyar bayan Cristiano Ronaldo da yake da kwallo 450.
Benzema a kakar bara a Real Madrid
Bayan tsohon kyaftin din kungiyar Sergio Ramos ya koma Kungiyar PSG, sai aka ba Benzema matsayin Mataimakin Kyaftin bayan Marcelo.
Benzema ya kasance wanda za a iya cewa ya dauki nauyin Kungiyar Real Madrid a kakar bara, inda ya rika zura kwallaye a duk lokacin da kungiyar take bukata har ta kai ga samun nasarar lashe Kofin Zakarun Turai.
A ranar 9 ga Maris din bara Benzema ya zura kwallo uku rigis a minti 17 a wasan zagaye na biyu a tsakanin Real Madrid da PSG yana mai shekara 34.
Da wannan zura kwallayen ne Benzema ya kafa tarinin wanda ya fi shekaru da ya zura kwallo uku rigis a Gasar Zakarun Turai.
Bayan nan Benzema ya ci gaba da zura kwallaye a kusan duk wasan Kungiyar Real Madrid, inda da zarar ba ya cikin wasa, magoya bayan kungiyar sukan shiga damuwa da rashin tabbas na samun nasara.
A ranar 30 ga Afrilun bara kuma da taimakon kwallayen da Benzema ya rika zurawa Real Madrid ta lashe Gasar La Liga karo na 35, inda ya zura kwallo daya a wasan da Real Madrid ta lallasa Kungiyar Espanyol da ci 4-0 a Filin Wasa na Bernabeu.
A Gasar Zakarun Turai kuma, a wasan farko na Kwata Fainal Real Madrid ta doke Chelsea da ci 3-1.
Da aka dawo wasa na biyu, sai Chelsea ta yi wa Madrid din shigar wuri inda ta ci kwallo 3, wanda ya jefa magoya bayan kungiyar a cikin fargaba da tsoro.
Ana cikin hakan ne Rodrigo ya farke kwallo daya, wanda hakan ke nufin kunnen doki, kafin Karim Benzema ya jefa kwallo a minti 96, inda suka yi waje da Chelsea, Madrid kuma ta tsallaka wasan dab da na karshe.
A wasan dab da na karshe, Real Madrid ta fafata da Kungiyar Man City, inda Benzema ya zura kwallo a ranar 4 ga Mayun bara daga fanareti wanda ya yi waje da Man City din, sannan ya tsallakar da Madrid zuwa wasan karshe, inda kungiyar ta doke Liverpool da ci daya mai ban haushi ta lashe kofin karo na 14.
A kakar bara, Benzema ya lashe kambun wanda ya fi zura kwallo a raga a Spain (Pichichi) da kwallo 27 a wasa 32, sannan ya zama wanda ya fi zura kwallo a Gasar Zakarun Turai da kwallo 15, sannan ya zama Gwarzon Dan Kwallon Gasar Zakarun Turai.
Fargabar da ake yi
Sai dai duk wadannan nasarori da ya samu, wasu na ganin kamar ba zai lashe kyautar ba ganin an samu kusan hakan inda Lewandowski ya samu nasarori da dama a shekara biyu a jere, amma Messi ya lashe kambun a bara.
Sai dai kuma ana mayar wa masu irin wannan martani da cewa a inda shi Lewandowski ya zura kwallaye da yawa tare da lashe Kofin Bundesliga kawai, shi Benzema ya lashe kusan komai kamar kofuna da yawan cin kwallaye a kaka daya.
Haka akwai batun girman kungiya, inda ake ganin kasancewar Benzema a Kungiyar Real Madrid za ta taimaka masa wajen lashe kambun.
Wani lamarin kuma shi ne ganin babu hamayya mai karfi a bana, inda baki daya babu Messi a ciki, shi kuma Ronaldo da yake ciki bai lashe ko kofi daya ba, sannan Kungiyar Man United ba ta tabuka abin a-zo-a-gani ba.
Kwallayen kawai ya ci, kuma ba su kai na Benzema ba.
Wani abu da zai taimaki Benzema shi ne garambawul da aka yi a tsarin zaben wanda zai lashe kyautar a bana, inda a sabon tsarin Gasar Kofin Duniya da za a buga ba za ta yi tasiri ba wajen lashe kambun na bana.
Yadda ake zaben Zakaran Ballon d’Or
A tsarin lashe kambun, ’yan jarida da masu horar da ’yan wasa da kyaftin-kyaftin na kungiyoyi da ayarin kasashe ne suke zaben.
Kowa zai zabi mutum uku, inda kowa ke da maki biyar.
Wanda mutum ya zaba na daya, zai samu maki uku, sannan na biyu da na uku su maki daya-daya, sannan a hada makin duka, wanda ya fi maki ne zai lashe kyautar.
A bara, ’yan jarida 180 ne suka yi zaben, amma a bana bayan gyare-gyare da aka yi, ’yan jarida daga kasashe da suke matakin na daya zuwa na 100 a jerin kasashen da suka nuna bajinta na FIFA za su yi zaben.