Balogun na shirin canza sheka
dan kwallon Najeriya Leon Balogun da yake buga wa kulob din Sb Darmstadt da ke Jamus ya bayyana cewa ba zai sabunta kwantaraginsa a kulob din ba. Kulob din Darmstadt dai ya samu hayewa rukunin gasar rukunin Bundesliga ta Jamus ne a kakar wasa ta bana amma duk da haka Balogun ya ce ba shi […]
dan kwallon Najeriya Leon Balogun da yake buga wa kulob din Sb Darmstadt da ke Jamus ya bayyana cewa ba zai sabunta kwantaraginsa a kulob din ba.
Kulob din Darmstadt dai ya samu hayewa rukunin gasar rukunin Bundesliga ta Jamus ne a kakar wasa ta bana amma duk da haka Balogun ya ce ba shi da niyyar sabunta kwantaraginsa a kulob din.
Balogun, wanda ya buga wa Najeriya Super Eagles wasa sau hudu kawo yanzu, yana daga cikin ’yan kwallon da suka buga wa kungiyar Super Eagles kwallo da Chadi a ranar Asabar da ta gabata a Kaduna.
Sai dai rahotanni sun ce akwai yiwuwar Balogun ya cigaba da yin kwallo Jamus a wani kulob bayan ya bar kulob din Sb Damstadt.