Balotelli ya sake komawa AC Milan
Shahararren dan kwallon nan Mario Balotelli ya sake komawa kulob dinsa na da AC Milan da ke Italiya a matsayin aro na shekara daya.Balotelli wanda ya zura kwallo daya kacal a kakar wasan da ta wuce a kulob din Liberpool ya koma AC Milan ne a matsayin na aro kamar yadda kungiyoyin biyu suka cimma […]
Shahararren dan kwallon nan Mario Balotelli ya sake komawa kulob dinsa na da AC Milan da ke Italiya a matsayin aro na shekara daya.
Balotelli wanda ya zura kwallo daya kacal a kakar wasan da ta wuce a kulob din Liberpool ya koma AC Milan ne a matsayin na aro kamar yadda kungiyoyin biyu suka cimma matsaya.
Balotelli dan shekara 25 ya sauka a Milan ne a ranar Talatar da ta wuce a garin San Siro don yi wa Milan kwallo a kakar wasa ta bana watau na 2015 zuwa 2016.
A lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a asibitin La Madonnina wajen da ake yi masa gwajin lafiya kafin ya sanya hannu a kwantaragin ya ce “na yi murna da na sake komawa kulob din Milan”.
“Na samu lafiya, abin da kawai nake bukata shi ne fara yin atisaye a kulob din da sauran takwarorina, don haka ba na son yin yawan surutu don ina so na fuskanci kakar wasa ta bana ne gadan-gadan don na samar wa kulob din Milan nasara”, inji shi.
Mario Balotelli dai ya yi wasa a kulob da dama ciki har da na Manchester City da na Liberpool da ke Ingila da na Inter Milan da AC Milan da ke Italiya.
A jiya Alhamis ne kulob din AC Milan da na Liberpool din suka cimma matsaya a kan dan kwallon.