Bam din Boko Haram ya hallaka mutum 20
Akalla mutum 20 ne suka rasu a wata fashewar bam da ta faru a karamar Hukumar Monguno da ke cikin Jihar Borno. Harin ya zo ne bayan da daruruwan mutanen garin da ’yan Boko Haram suka kora sun koma gidajensu, bayan da sojoji suka kwato shi daga mayakan Boko Haram din. Mutanen Monguno na murnar […]
Akalla mutum 20 ne suka rasu a wata fashewar bam da ta faru a karamar Hukumar Monguno da ke cikin Jihar Borno. Harin ya zo ne bayan da daruruwan mutanen garin da ’yan Boko Haram suka kora sun koma gidajensu, bayan da sojoji suka kwato shi daga mayakan Boko Haram din.
Mutanen Monguno na murnar da farin cikin komawa garin nasu ne wasu bama-bamai da ake zargin mayakan Boko Haram sun gudu sun bar su suka tashi inda suka hallaka mutanen da aka ambata tare da jikkata wasu. Wani dan Sibiliyan JTF a garin da lamarin ya faru a kan idonsa mai suna Modu Kachalla ya shaida wa wakilinmu cewa, “Yau muna raye-raye da kade-kade don murnar mun dawo garinmu bayan cin nasarar korar Boko Haram, sai muka ji tashin bam, inda ya kashe mutane tare da jikkata wasu, mun kai su asibiti a cikin garin Maiduguri.”
Wani da ya bayyana sunansa da Malam Ibrahim, cewa ya yi “Muna cikin bikin murna da farin ciki ke nan sai wani dan banga ya gano maboyar bama-bamai ya dauko ya kai wani wuri ya ajiye, can sai muka ji wadannan bama-bamai sun tashi sun kashe mana mutane da jikkata wasu.”