Bam ya hallaka mutane 10 a Istanbul

A ranar Talatar da ta gabta ne hukumomi a kasar Turkiyya suka ce mutane akalla 10 ne suka mutu bayan wasu bama- bamai sun tashi a wani yanki da masu yawan bude ido suka fi zuwa da ke birnin Istanbul, babban birnin kasar.Bama-baman sun fashe ne da misalin karfe 10 na safe a agogon kasar […]

Bam ya hallaka mutane 10 a Istanbul
Bam ya hallaka mutane 10 a Istanbul

A ranar Talatar da ta gabta ne hukumomi a kasar Turkiyya suka ce mutane akalla 10 ne suka mutu bayan wasu bama- bamai sun tashi a wani yanki da masu yawan bude ido suka fi zuwa da ke birnin Istanbul, babban birnin kasar.
Bama-baman sun fashe ne da misalin karfe 10 na safe a agogon kasar a yankin Sultanahmet kusa da masallacin nan mai suna, Blue Moskue.
Wani bayani da aka wallafa a shafin Intanet na gwamnan birnin ya ce mutane 15 ne suka jikkata.
Wasu rahotanni sun ce ‘yan kunar-bakin-wake ne suka tayar da bama-baman ,kodayake, ba a tabbatar da rahotannin ba tukuna.
Shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ya dora alhakin harin ’yan kunar bakin wake da suka fito daga kasar Siriya, wadda take makwabtaka da ita. Kodayake, ba a samu wata kungiya da ta ce ita ce ta dauki alhakin harin ba zuwa lokacin hada wannan rahoton.