Bam ya kashe 28 a Turkiyya

A shekaranjiya Laraba ne wani bam da aka dana cikin mota a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya ya hallaka akalla mutane 28 da kuma jikkata wasu fiye da 60.Jami’ai sun ce bam din ya tashi ne a lokacin da motocin safa- safa na sojoji suka tsaya a inda ake ba da hannu da ke kusa […]

Bam ya kashe 28 a Turkiyya
Bam ya kashe 28 a Turkiyya

A shekaranjiya Laraba ne wani bam da aka dana cikin mota a Ankara, babban birnin kasar Turkiyya ya hallaka akalla mutane 28 da kuma jikkata wasu fiye da 60.
Jami’ai sun ce bam din ya tashi ne a lokacin da motocin safa- safa na sojoji suka tsaya a inda ake ba da hannu da ke kusa da majalisar dokoki da kuma hedkwatar sojoji.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan wanda ya soke tafiyarsa zuwa kasar waje ya sha alwashin ci gaba da yaki da wadanda suke kaddamar da hare-haren da kuma wadanda suke goya musu baya.
Wata majiyar tsaron a kasar ta zargi kungiyar ‘yan awaren kurdawa ta PKK da aka haramta.
Kuma a jiya Alhamis ne Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya yi alkawarin daukar fansa kan wadanda suka kai harin.
Sakatare Janar na kungiyar Tsaro ta NATO Jens Stoltenberg ya ce ya kamata kawayen NATO su tsaya kafada da kafada a yakin da ake yi da ta’addanci. Ga alama ya fadi hakan ne saboda Turkiyya na cikin kasashen kungiyar.