Bam ya kashe mutum 25 a Libya
Akalla mutane 25 ne suka rasa ransu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon wani tashin wani babban bam a Tripoli, babban birnin kasar.Fashewar bam din dai, wanda ya faru a garin Garabulli, ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin mutanen garin da mayakan sa-kai daga birnin Misrata.Da farko dai, wasu jami’ai a […]
Akalla mutane 25 ne suka rasa ransu sannan wasu da dama suka jikkata sakamakon wani tashin wani babban bam a Tripoli, babban birnin kasar.
Fashewar bam din dai, wanda ya faru a garin Garabulli, ya biyo bayan wata arangama da aka yi tsakanin mutanen garin da mayakan sa-kai daga birnin Misrata.
Da farko dai, wasu jami’ai a kasar sun shaida wa manema labarai cewa al’amarin ya faru ne a wani wurin ajiyar makamai, kamar yadda BBC ta bayyana.
Sai dai wani mazaunin garin Garulli ya ce wata babbar mota ce cike da abubuwan fashewa ta tarwatse.
A makon watan nan ne dai masu yaki da IS, wadanda suke hadin gwiwa da gwamnatin Libyar da ke da goyon bayan Majalisar dinkin Duniya a Tripoli, suka ce sun kwace ikon gabar tekun Sirte daga hannun mayakan IS.
Sirte dai shi ne babban gari da ke karkashin ikon IS baya ga Iraki da Siriya.