Bam ya kashe mutum 4 da jikkata wasu a Borno
Fasinjoji hudu kuma sun sami raunuka daban-dabam kuma nan da nan an kai su babban asibitin Biu don yi musu jinya.

Aƙalla fasinjoji huɗu ne suka mutu yayin da wasu huɗu suka jikkata sakamakon fashewar wani bam a ƙarƙashin wata motar fasinja a ƙaramar hukumar Biu ta Jihar Borno.
Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta tabbatar ta afkuwar lamarin.
- Gobara ta kashe ɗan shekara 7 a sansanin ’yan gudun hijira
- ’Yan bindiga sun yi garkuwa da jami’in FRSC a Benuwe
Majiyoyin leƙen asiri sun shaidawa Zagazola Makama cewa, lamarin ya faru ne a ranar 19 ga Maris, 2025, da misalin ƙarfe 2:30 na rana a lokacin da wata mota ƙirar Golf 3 ta Wakil Fari ta tashi daga garin Kimba zuwa garin Biu.
Bayan sun isa mahaɗar Sabon Garin Kimba, motar ta taka wata nakiya (IED), wanda ya kai ga fashewa da ta kashe fasinjoji mata uku da fasinja namiji guda nan take.
Majiyar na cewar wasu fasinjoji hudu kuma sun sami raunuka daban-dabam kuma nan da nan an kai su babban asibitin Biu don yi musu jinya.
Daga bisani likitoci sun tabbatar da mutuwar wadancan mutane huɗu sannan aka ajiye su a ɗakin ajiyar gawa na asibitin kafin a miƙa su ga ’yan uwansu don yi musu jana’iza.
Bincike na farko ya nuna cewa ’yan ta’addar ISWAP ne suka dasa waɗannan bama-bamai (IEDs) a tunanin sojoji za su taka.
Jami’an soji sun tabbatar da faruwar hakan, tare da duba ƙarin barazanar da ake fuskanta daga wadannan ‘yan ta’addan don tabbatar da tsaro ga masu amfani da hanya.
Hukumomi sun kuma ƙaddamar da gangamin wayar da kan al’umma kan haɗarin bama-bamai da ba su fashe ba, don kaucewa faruwar lamari irin ya hakan.