Bam ya kashe sojojin Kamaru biyu
A shekaranjiya Laraba ne rahotanni daga lardin Arewa-mai-Nisa na kasar Kamaru na cewa sojojin kasar biyu sun mutu sakamakon fashewar wata roka a cikin motar da ta dauke su. Wakilin kafar yada labarai ta BBC ya ce lamarin ya faru ne a garin Bodo da yake yankin Logone da Chari na lardin. Wakilin ya kara […]
A shekaranjiya Laraba ne rahotanni daga lardin Arewa-mai-Nisa na kasar Kamaru na cewa sojojin kasar biyu sun mutu sakamakon fashewar wata roka a cikin motar da ta dauke su.
Wakilin kafar yada labarai ta BBC ya ce lamarin ya faru ne a garin Bodo da yake yankin Logone da Chari na lardin. Wakilin ya kara da cewa baya ga sojojin, akwai wasu 23 da suka samu rauni sakamakon lamarin.
Har yanzu dai ba a san wannan ya dasa rokar a cikin motar ba, sai dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-hare a kasar.
Har ila yau, ’yan gwagwarmayar suna ci gaba da rike wasu garuru da ke kan iyakar Najeriya da Kamaru, ciki har da dajin Sambisa da tsaunin Mandara. Kodayake a kwanakin baya, dakarun Kamaru da na kasar Chadi sun yi nasarar kwato wasu garuruwan daga hannunsu.