Bam ya kashe wani yaro dan gudun hijira a Borno

Tashin bam ya kashe wani yaro dan shekara 13 a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno. Yaron ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake wasa da wani bam din da ya ki tashi da aka dawo da shi daga karamar hukumar Bama, a ranar Litinin. Fashewar bam din a sansanin ‘yan gudun hijirar […]

Bam ya kashe wani yaro dan gudun hijira a Borno

Sansanin ‘yan gudun hijira da ke Karamar Hukumar Ngala lokaci da wata gobara ta tashi

Tashin bam ya kashe wani yaro dan shekara 13 a sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.

Yaron ya gamu da ajalinsa ne yayin da yake wasa da wani bam din da ya ki tashi da aka dawo da shi daga karamar hukumar Bama, a ranar Litinin.

Fashewar bam din a sansanin ‘yan gudun hijirar da ke karamar hukumar Jere ta kuma raunata karin wasu mutum uku.

Hukumar ba da Agajin Gaggawa ta Kasa (NEMA) ta tabbatar da faruwar lamarin.

Sanarwar ta ce wadanda suka samu raunin bam din na samun kulawa a Asibitin Kwararru na Jihar Borno.