Bam ya tarwatsa manomi a Neja
Wani manomi mai suna Isyaku Gambo, ya rasa ransa bayan da wani bam ya tashi a kusa da garin Bassa, da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Wani manomi mai suna Isyaku Gambo, ya rasa ransa bayan da wani bam ya tashi a kusa da garin Bassa, da ke Ƙaramar Hukumar Shiroro a Jihar Neja.
Mazauna yankin, sun ce lamarin ya faru ne yayin da manomin ke kan hanyarsa ta kai kayan amfanin gona zuwa Bassa a babur ɗinsa.
- Jam’iyyar NPP mai mulki ta amince da shan kaye a Zaɓen Ghana
- ’Yan bindiga sun kai wa mahaifiyar Gwamnan Taraba hari
Ana zargin cewa ’yan ta’adda ne suka dasa bam ɗin a kan hanya tsakanin Unguwan-Usman da Bassa.
Wani mazaunin yankin, ya bayyana cewa fashewar bam ɗin ta tarwatsa gawar mamacin gaba ɗaya.
“Lamarin ya faru ne a yau (Asabar) da misalin ƙarfe 3 na rana.
“Mamacin na kan hanyarsa ta dawowa daga gona bayan ya ɗauko kayan amfanin gona.
“Wannan ne karo na farko da muka fuskanci irin wannan a nan. Ana zargin ’yan ta’adda ne suka dasa bam ɗin,” in ji wani mazaunin yankin.
Ƙoƙarin samun ƙarin bayani daga kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ci tura domin bai amsa kiran waya baya.
Har ila yau, Kwamishinan tsaron cikin gida na Jihar Neja, Birgediya Janar Bello Abdullahi Mohammed (mai ritaya), ba a same shi a waya ba, kuma bai dawo da amsar saƙon da aka tura masa ba.