Bam ya tashi a garin Maiha
Bam ya kashe mutum daya kuma mutum biyu sun samu rauni a garinLugda da ke karamar Hukumar Maiha a Jihar Adamawa. Ana zargin ’yan bindiga ne suka saka bam din, kuma rahotanni sun ce marigayin da wadanda suka samu rauni hakan ya faru da su ne suna shan dumin wuta saboda sanyi da ake yi.Majiyarmu […]
Bam ya kashe mutum daya kuma mutum biyu sun samu rauni a garinLugda da ke karamar Hukumar Maiha a Jihar Adamawa.
Ana zargin ’yan bindiga ne suka saka bam din, kuma rahotanni sun ce marigayin da wadanda suka samu rauni hakan ya faru da su ne suna shan dumin wuta saboda sanyi da ake yi.
Majiyarmu ta ce wajen neman makamashi ne sai daya daga cikinsu ya hangi bakar leda a ajiye ba tare da sanin cewa akwai bam a cikinta ba.
Marigayin bai san da bam a cikin ledar ba sai ya dauke ta zai saka a wuta, nan ne bam din ya tashi ya tarwatse da shi sauran biyun suka samu rauni aka kai su Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Yola.
Kakakin ’Yan sandan Jihar Adamawa, Malam Abubakar ya ce, lamarin ya faru ne sakamakon rashin sani, inda mutanen ba su duba abin da ke cikin ledar ba.
Ya bukaci mutane su kiyaye kuma su zama masu lura kafin su taba abubuwan da ba su sani ba. Kuma idan suka ga wani abu da suke shakka su yi kokari su sanar da ’yan sanda don kauce wa aukuwar irin haka.