Bam ya yi ajalin ɗaliban Islamiyya 2 a Abuja
Rundunar ta ce ta gano wasu mutum uku ne da suka kawo bam ɗin makarantar.
Wani bam ya tashi a makarantar Islamiyya ta Sani Uthman da ke Kuchibuyi a Ƙaramar Hukumar Bwari a Abuja, inda ɗalibai biyu suka rasu, sannan wasu huɗu suka jikkata.
Lamarin ya faru da misalin ƙarfe 11 na safiyar ranar Litinin.
- Mamakon ruwan sama ya haddasa ambaliya a Saudiyya
- ’Yan sanda sun ceto yara 4 da aka sace daga Bauchi a Anambra
Kakakin rundunar ’yan sandan Abuja, SP Josephine Adeh, ta ce, “Bincike ya nuna cewa wasu mutum uku ne daga Katsina suka kawo bam ɗin makarantar.
“Mutum biyu daga cikinsu sun mutu yayin da suke ƙoƙarin gyara bama-bamai, yayin da mutum na uku da wata ‘yar kasuwa suka ji munanan raunuka kuma ana kula da su.”
Tawaga ta musamman ta rundunar ’yan sandan Birnin Tarayya, ta tabbatar cewa bam ne ya tashi.
Haka kuma, SP Adeh ta ce an kama mai makarantar, Mallam Adamu Ashimu, domin yi masa tambayoyi.
Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa, “Wani ɗalibi, wanda ya shiga makarantar a ranar 3 ga watan Janairu, 2025, ne yake ɗauke da bam ɗin lokacin da ya tashi.
“Kuma bam ɗin ya jikkata wasu ɗaliban kuma ya jawo tashin hankali a makarantar.”
Rahotanni sun bayyana yadda mutane a yankin suka shiga mummunan tashin hankali bayan fashewar bam ɗin, inda iyayen yara da al’ummar yankin suka taru suna ƙoƙarin gano abin da ya faru.
Wasu daga cikin iyayen sun bayyana damuwarsu kan rashin tsaro da kuma yadda makarantu suka zama wuraren da ake kai wa hari.
Kwamishinan ’yan sandan Birnin Tarayya, CP Olatunji Disu, ya ja kunnen jama’a su kasance masu lura da tsaro kuma su rika bayar da rahoto duk wani abun zargi.
Ya kuma ƙara jaddada aniyar rundunar wajen daƙile irin waɗannan hare-hare a nan gaba.