Bama-bamai sun tashi a kotunan Ribas biyu
Rikicin siyasa da ke addabar Jihar Ribas ya dauki sabon salo a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka sanya bama-bamai a manyan kotunan jihar biyu lamarin da ya hana kotunan biyu suka kasa zama don shari’ar wasu muhimman al’amura tare da kone […]
Rikicin siyasa da ke addabar Jihar Ribas ya dauki sabon salo a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka sanya bama-bamai a manyan kotunan jihar biyu lamarin da ya hana kotunan biyu suka kasa zama don shari’ar wasu muhimman al’amura tare da kone fayil-fayil din shari’un.
Kotunan da suka hada da Babbar Kotun da ke Ahoada da Babbar Kotun Okehi suna sauraron shari’un siyasa ne da suka shafi bangaren da Gwamna Rotimi Amaechi ke goyon baya da wanda Fadar Shugaban kasa ke mara masa.
A Ahoada, an kefa bama-bamai biyu cikin harabar kotun da sanyin safe, kuma daa daga cikinsu ya fashi tare da kama wuta inda ta shafi sassan ginin kotun kamar yadda shaidu da mahukunta suka ce.
Shaidu sun ce daa daga cikin bama-baman ya fashe a harabar ginin kungiyar Lauyoyi ta kasa da ke ciki kotun inda ta kone wani bangarensa, yayin da aka iske dayan a kusa da ginin babbar kotun inda ’yan sanda suka lalata shitesses said one of the debices edploded at the Nigerian Bar Association (NBA) building within the court ypremises and razed down part of it, while the other one was found close to .
Sai dai babu wanda bama-baman suka kashe ko suka raunata, amma kotun ta kasa zama a ranar don sauraron shari’ar.
Babbar Kotun Ahoada a karkashin Mai shari’a Charles Wali an shirya za ta yi zaman sauraron karar da Shugaban Majalisar Jihar Dan Amachere da mambobi 24 suka shigar ne kan mambobi shida da suka yi tawaye a karkashin Mista Ebans Bipi, wanda a bara ya yi da’awar zama shugaban majalisar yana jagorantar ’yan majalisar da suke adawa da Gwamna Amaechi ne.
An hakikance suna goyon bayan abokin gabar siyasar Amaechi ne Ministan Ilimi Nyesom Wike da ke samun goyon bayan Fadar Shugaban kasa.
Wannan ne karo na biyu da bam ya tashi a harabar kotun, sai dai harin na Litinin ya jawo hankali ne ganin saura awanni kotun ta zauna kan shari’ar ’yan majalisar. A watan jiya wani abin da ake zargin bam ne ya fashe a garejin kotun.
A Babbar Kotun Okehi da ke karamar Hukumar Etche an samu rahoton tashin wuta a harabar kotun. Wata majiya a kotun ta shaida wa wakilinmu cewa wuta ta kone wasu muhimman takardun shari’a da sauran muhimman takardu.
A shekarar 2012, Babbar Kotun Okehi ta saurari shari’ar takaddamar PDP a tsakanin Cif Godspower Ake da Mista Felid Obuah, inda ta ce halattaccen shugaban jam’iyyar shi ne Ake, da Wike da uwar jam’iyyar ta kasa ke mara masa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Ribas ta la’anci harin na Ahoada tare da bayyana shi da karami da ba zai iya jawo mummunar barna ba, kamar yadda kakakin rundunar Ahmad K. Muhammad ya fada a wata sanarwa.
Gwamnatin Jihar da Jam’iyyar APC sun zargi PDP da tashin bama-baman, yayin da ita PDP ta zargi gwamnatin jihar kan tashi bama-baman.