Bambamin bilinbituwar birkitattun batutuwan barkwanci
Bambamin baka Burgar burge mutumin bukka Shaci-fadin sa shakku Walwalar mai tsigi da tukku Bututun batun raraka Daga Lantsadan aka zo da akwaku Baban-bakin ce-ce-ku-cen Birtaniyawa Ya hada takarar kokowa Har da uwargida mai dawa Tumbin-Giwa akai kamun kazar kuku Yaren yarfin yarfe Yawar yagalgala yafe Yaki da yunwa ake wa dafe-dafe Yankwanewar […]
Bambamin baka
Burgar burge mutumin bukka
Shaci-fadin sa shakku
Walwalar mai tsigi da tukku
Bututun batun raraka
Daga Lantsadan aka zo da akwaku
Baban-bakin ce-ce-ku-cen Birtaniyawa
Ya hada takarar kokowa
Har da uwargida mai dawa
Tumbin-Giwa akai kamun kazar kuku
Yaren yarfin yarfe
Yawar yagalgala yafe
Yaki da yunwa ake wa dafe-dafe
Yankwanewar laulayi a daddafe
Yamutsin yakicewa a kife
Taro ya cika ya batse
An yi tande-tande an gyatse
’Yan takara sun kotse
Masu akwaku sun hantse
Da kammalawa kowa ya waste
Birkitattun batutuwa
Birgimar bagararwa
Bini-binin bilinbituwa
Basajen bututun busawa
Banga-bangar bubbugawa
Babban bakin ce-ce-ku-ce
Yai takaddama makon da ya arce
Maza karamin lauje da mace
Hana masu ciki mace-mace
Farfado da farfajiyar ilimin da ke mace
’Yan takara
Da masu taka-kara
Su kai ta kara
Wajen bijiro da batutuwa karara
An dai karkare ba harara
Gunsar gintsewar gyatsa
Mai fuka-fukin tashi yai kwankwatsa
Kallabin rawuna tai gatsine gatsa-gatsa
Da Uban masu kwankwatsa
Ya yunkura kamun kifi da fatsa
Birnin Dabo
Kun san ba a dabo
Balle zari ruga da kwabo
Tsoho da sabo
Gwamnati ba ta sabo
Kun dai tallata manufofi
Ku bar yi wa juna yarfi
Kar ku maishe da talakawa makafi
Nagarta an fasko wanda ya fi
Masu ji da na-zomo sun yi tafi
Mu dai mun taru a shigifa
farfajiyar jami’a mai rumfa
Babban-bakin-ce-ce-ku-ce yai musaffa
Daga Lantsandan aka bude kafa
Haurobiyawa a dai yi kaffa-kaffa
Gwamnan gundumar gandun aiki
Gararumar gyaran girki
Ginsamin gwabjejen miki
Gangamin ban mamaki
Gwanintar gujewar mai mulki
An tuna da almajirai
Da talakawa fakirai
Inganta rayuwar jarirai
Murmurewar uwar-jiki ceton rai
A dai gyara kura-kurai
Za a hana dirshan din kashe fatarai
Kwayoyi sun jefa gayu hadari
’Yan lalle da Adon-gari
Kui aiki nagari
Kar ku afka garari
A daina kaso-kason wawanci
Damfarar damalmala kasuwanci
Cinikin ci-mu-ci
Carafken ci da gumjn mai kawaici
An dan jinka masa tukuici
Damo-da-kura-da-diyya
Dama-damar-kurda-kurdar-tsiya
Jam’iyyun jar-miyya
Jimamin jin jikin juriyyar jiniya
Daura damarar daukar dawainiya
Masu fuka-fukin tashi
Kar ai muku wa-ka-ci-ka-tashi
Kuna ta tsimayin kwasar adashi
Zakuwa ta sa ku hanzarin tashi
Mulki na biya ba bashi
Budurwa ai mata toshi
Daushen goro sa bakin tsohuwa washi
Maigida kar ka hada kashi
Cefane ke sa uwargida karsashi
Ta gama tai kwalliya da kunshi
Saisaita salon siyasa
Sunce sasarin sa-in-sa
Sasanta sabanin rashin sani
Sahalewar al’umma aiki da sani
Sarewar sanyaya saiwoyin sassa
Asibicin makon da ya arce, wato ranar karamin lauje ga watan Fafe-baure na shekara ta dubu karamin lauje da sili da manuniyar kasa, Babban-bakin-ce-ce-ku-cen Birtaniya ya shirya karon-battar kalallame kalaman ’yan takarar Gwamnan Jihar Tumbin-giwa a shigifar farfajiyar Jami’ar Mai martaba na birnin Dabo, cikin wata katafariyar rumfa da zimmar ganin ba a yi wa mutane rufa-rufa ba.
’Yan takara da masu taika-karar da aka gayyato sun hada da Mai fuka-fukin tashi da ya yi GUMTSAR GINTSEWAR GYATSA, sai Malam TATTAKIN-TAKUN-KAI, da MUMINAR MANAGARCIYAR MACE MAI MANUFA, wato Uwargida Gwamna Gwamma Gwaggon al’umma. Daukacin wadannan ’yan takara da jam’iyyunsu na hankoron darewa bisa karagar mulkin Jihar Tumbin-giwa a birnin Dabo, inda ba a dabo.
Daukacin mumbarin kowane/kowace dan/’yar takara an alamta alamun al’adun al’umma, ko in ce tambarin jam’iyya.
Wani abin ban ta’ajibi shi ne daukacin mutanen da suka tafka takaddama a shigifar jami’a, sun bibiyi kadin tsilli-tsillin matsalolin al’umma, wadanda suka hada da yadda za a inganta farfajiyar Bokan Turai da harkokin koyon watsattsake da fallen shafukan wagagen littattafai. Kusan kowane daga jerin wadanda suka fafata a takaddamar ce-ce-ku-cen da zarar ya/ta fara kwakwazo kai ka ce da an mika musu ragamar mulki, shi ke nan al’umma za ta ci AWARA TA WARWARE. Ga dukkan alamu dai sai an gwada akan san na-kwarai. Masu wasan Samson-siya-siya da kwakwalwar talakawa a daina zuki-ta-malle kama-kare ka hada shi da zomo.
Babban abin takaici dai a wannan takaddamar ce-ce-ku-ce da aka tafka, shi ne kin halartar Gwamnan Gundumar Gandun aiki; sai kuma daukacin ’yan takarar da ke hankoron darewar karagar mulki, kusan duk a cikin birni za su aiwatar da tsare-tsaren ayyukansu. Saboda haka sai mu ce al’ummar karkara ko oho!
Sannan babu wani daga jerin jam’iyyun jar-miyya da ya kudiri koyi da kyawawan manufofin Baban-burin-huriyya, musamman yadda gwamnati mai ci ke ta fafutikar dundume kururun ’yan dugwi-dugwi da ke kwankwadar fura-mai-kyau a farfajiyar koyon watsattsake da buda wagagen littattafai matakin farin-farawa. Shirin kawar da dirshan din kashe fatari a tsakanin masu fuka-fukin tashi, musamman wadanda aka yaudare su suke ta zuba adashin, ranar kwasa sai a jinka musu jagwalgwalon sa-in-sar siyasar jagaliya
Batu na ingarman karfen karafan titin tarragon layin dogo, ba tare da bata lokacin wulwulawar hannayen agogo ba, duk wani dan takara da ya yi tuya ya manta da albasa mai lawashi, tabbas sai mu ce daukacin batutuwansa/ta an karke ne kawai da BIRKITATTUN BATUTUWAN BILINBITUWAR BARKWANCI. Kuma nagartar kowane dan takara tuni Haurobiyawa sun fasko, don haka babu wanda zai cusa musu duhun kurungu a sako.