Bambance-bambancen da ke tsakanin namiji da mace

Duk lokacin da ake magana kan bambanci a tsakanin namiji da mace, ana magana ce a kan bambancin da tsarin halitta ya haifar  ba don wani jinsi ya fi wani  jinsi ba. Halitta ce ta samar da haka, wannan ne ya sa suke  zama tare, ba tare da sun gaji  da juna ba, kuma halittar […]

Bambance-bambancen da ke tsakanin namiji da mace

Bambance-bambancen da ke tsakanin namiji da mace

Duk lokacin da ake magana kan bambanci a tsakanin namiji da mace, ana magana ce a kan bambancin da tsarin halitta ya haifar  ba don wani jinsi ya fi wani  jinsi ba. Halitta ce ta samar da haka, wannan ne ya sa suke  zama tare, ba tare da sun gaji  da juna ba, kuma halittar ce ta dora wa kowane nauyin da ya fi  dacewa  da shi. Don haka, ga abin da masana halayyar dan Adam da malamai da kuma likitoci suka bayyana dangane da bambancin da ke tsakaninsu don a fahimci yanayinsu da irin rawar da kowanensu zai iya takawa a rayuwarmu ta yau da kullum.

Tsarin halitta: Idan muka dauki girman jiki da tsawo, mafi  yawa  mata kananan jiki ne da su, maza kuma sun fi girman jiki, yawancin mata gajeru ne a kan maza. Sautin muryar namiji tana da girma,  ita kuma mace muryarta siririya ce. Mace ta fi namiji saurin girma, domin tun tana cikin  mahaifa, mace ta fi garkuwar kamuwa da cututtuka.  Haka mace tana  riga namiji saurin balaga, kuma tana  riga namiji  daina  haihuwa. Huhun namiji ya fi na mace zukar iska. Haka nan ita kanta kwakwalwar namiji ta fi ta mace zukar iska. Haka ita kanta kwakwalwar namiji ta fi ta mace girma. Zuciyar namiji ta fi saurin bugawa  a kan ta mace.

Halayya: A halayya kuma masana sun yi amanna cewa, namaiji   ya fi mace son aikin karfi, da gwagwarmaya, mace kuwa ta fi son tafiyar da komai a hankali. Mace ba ta iya yanke shawara a gurguje, kamar yadda  namiji kan yanke nan take. Wannan dalili ne ya sa da wuya ka ji mace ta rataye kanta, ita ta gwammace ta sha guba, ko wani magani da zai hallaka ta nan take wanda bai taka kara ya  karya ba, shi kuwa namiji hakan bai zama abin a zo a gani a wajensa ba.

Mace ta fi son kwalliya da duk wani abin da zai kayatar  da ita,  fiye  da namiji, haka mace ta fi namiji surutu, kuma ta fi namiji kula da yara, ita hankalinta a kullum a kan ci gaban  iyali yake, kuma ita mace ba ta iya boye sirri kamar yadda namiji yake boyewa. Mace ta fi namiji  saurin kuka,  ta yadda za ka ga cewa abu kadan zai iya sanya mace kuka.

Zamantakewa: Masana sun ci gaba da cewa sha’awa ce ke sa namiji son mace, amma shi namiji muhimmancinsa ne ke sa mace sonsa. Burin namiji shi ne ya samu macen da zai iya iko da ita, ita kuwa a kullum so take ta samu mai kaunarta, mace ta fi son ganin jarumtar namiji, shi kuwa  kwalliya da kyan mace su ne a gabansa. Duk matsayin da mace take ciki tana  iya boye son jima’i fiye da namiji.

Bincike ya tabbatar da cewa da a ce mace tana da kamanni irin  na namiji da halayya irin tasa da ba za ta iya ba shi sha’awar da zai ja ta gare shi ba, ballantana ma har su iya zama tare su yi mu’amala irin ta auratayya tare.

Na binciko wadannan bambance-bambance ne don a fahimci  yanayin kowa da  irin rawar da kowanensu zai iya takawa, saura da me? Allah Subhanahu Wa Ta’ala Yana cewa a cikin Alkur’ani “Ba Mu halicci mutum da aljani ba sai don su bauta Min.” Ka ga ke nan, akwai matukar bukatar mu kyautata alakar da ke tsakanin namiji da mace, musamman a zamantakewar aure, domin gyaruwarta ce gyaruwar al’umma, Allah Ya agaza mana.

 

Za a iya samun Ibrahim Hamisu ta: 080 60651676              Email: [email protected]