Gasar Rubutu ta Aminiya ta bambanta da sauran —Dokta Aliya
5 ga Yuni, za a bayar da kyaututtuka ga gwarazan gasar 2020.
A ranar Asabar, 5 ga Yuni 2021 za a karrama gwarazan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Aminiya da kyatuttuka.
Dokta Aliya Adamu tana cikin masanan da suka yi alkalanci a Gasar kuma wakilinmu ya zanta da ita a kan abubuwan da suka shafi gasar da sauransu.
- El-Rufai na cijewa za mu yi yajin aikin gama-gari —NLC
- Mata sun yi zanga-zangar neman a halasta karuwanci
A matsayinki na malamar jami’a kuma daya daga cikin alkalan Gasar Rubutu ta Aminiya me za ki ce a kan gasar?
Da farko dai sunana Aliya Adamu Ahmad, ni ’yar Sakkwato ce, a nan nake zaune, kuma malama a Jami’ar Jihar Sakkwato a bangaren Nazarin Harsunan Najeriya.
Ina cikin wadanda suka ji dadi da Kamfanin Buga Jaridu na Media Trust mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya ya shigo cikin harkar inganta adabi. Saboda gasar hanya ce ta inganta rubutu.
In aka ce fitaccen kamfani ko fitacciyar jarida irin Aminiya sun fito da tunanin inganta adabi a matsayina na daliba, malama, mai koyarwa a makaranta a fannin Nazarin Harshe da Adabi, ina ganin kamfanin ya yi daidai, ya yi namijin kokari ya yi abin a yaba, ina fata a ce yanzu aka fara.
Wace rawa kike ganin gasar za ta taka wajen bunkasa Adabin Hausa?
Duk abin da za a yi aka sanya shi a fannin gasa, to abin an yi masa mazauni mai kyau.
Abu na farko da yake sawa a samu ingantaccen sakamako a sanya shi a fannin gasa.
Sanya shi a matsayin gasa nufin mutane su shiga kowa ya gwada fasaharsa da baiwar da Allah Ya ba shi, wanda bai iya ba, ba zai shigo ba don kuwa iyawa ce ke haifar da abin kwarai a cikin bibiyar doka kowa zai samar da abu mai kyau.
A nan ake taskacewa a fitar da abu mafi kyau daga nan an samar wa abin mazauni mai sahihanci da inganci.
A matsayinki na daya daga cikin alkalan gasar yaya za ki kwatanta ingancin labaran da kuka tantance?
Labarai ne masu inganci domin sun bi dokar rubutu, ba kowa ne zai iya rubutu ba, domin yana da dokoki dole sai ka samu ilimin rubutu ko da kai mai fasaha ne ta wata baiwa ko kirkira sai ka hada su ne tafiyar take zama mai inganci.
Kusan labaran da na duba ba wanda marubucinsa bai yi rawar gani wajen samar da shi da kwarin gaske ba.
Lokacin da kika samu gayyatar Aminiya cewa kina cikin alkalan gasar yaya kika ji?
Na ji dadin gayyatar saboda in an ce an zabe ka cikin mutane an ga wani abu a tare da kai ne na inganci, shi ya sa aka ce ka zo ka yi.
Ta yiwu masu hannu a shirya gasar ta Aminiya sun san dan kokarin da na yi a wasu gasannin da na yi alkalanci.
Ta yiwu haka ya sa aka gayyato ni, ina godiya. Ba wannan ne karo na farko da kika yi alkalanci a gasar rubutu ba, yaya za ki kwatanta wannan gasa da ta baya?
Kusan tafiyar guda ce, misali gasar BBC da ta Kungiyar Marubuta Mata da wasu gidauniyoyi.
Amma akwai bambanci da na Aminiya Trust da wadancan da na fara yi wa alkalanci.
Me ya fi burge ki a wannan gasa?
Abin da ya fi burge ni, shi ne yadda aka dauki batu ko taken labari daya, sabanin wadanda ake barin labari a bude kowa ya dauki taken da yake so daga cikin abubuwan da ke faruwa a cikin al’ummarsa a yi musu alkalanci.
A na Aminiya sai aka dauki maudu’i daya wato siyasa wadda tana cikin muhimman abubuwan rayuwarmu.
Domin duk inda muke muna tare da siyasa ko ba ta gwamnati ba, a sauran mu’amalolin rayuwarmu, ko addini da al’ada.
Hakan ya burge ni yadda aka kayyade cewa gasar za ta yi magana ne a kan siyasa, alkalamin duk wanda zai shiga a kan siyasa zai yi Magana.
In za a rika daukar abu daya a yi lugudensa gasa za ta rika inganci domin an san inda aka dosa a wurin warware duk wani abu da marubuci ya shigo da shi na kalubale.
Da yawa in ana tafiya irin ta masu ilimi za a samar da rubutun da zarensa da aka ja ya bambanta da sauran, ko an samu a gasar Aminiya?
Ina son in mayar da mu baya kadan a kan alkalacin gasa da na yi a baya, wato a Gasar HIKAYATA, a lokacin da aka aiko min da rubutun gasar an aika wa wadansu alkalai guda biyu wadanda ban sani ba, kuma ban taba ganinsu ba.
Bayan mun gama alkalanci mun aiko da sakamako sai aka gayyace mu zama, kowa ya zo da labaran da ya tantance ya kuma fadi yadda ya yi aikinsa.
Karo na farko da muka hadu da abokan aikin mun san sunayen juna ne kawai a kafafofin sada zumunta, amma sai hukuncinmu ya zama daya duk da hanyoyin sun bambanta, labari daya muka zaba.
Mun yi farin ciki da haka tare da ganin in za a ci gaba da daukar hanyar tura wa alkalan gasa rubutu ba tare da sanin kowa ba, gudun hada tunani. Wannan hanya ce mai kyau da inganci, haka aka yi a gasar rubutu ta mata, sai ga wannan ta Aminiya, su ma haka suka yi.
Sai bayan kammalawa na san alkalan kuma labaran da na zaba su ma su suka zaba.
Gaskiya wannan hanya ce ta masu shirya gasa, amma na so kafin fitar da sakamako mu hadu da juna kamar yadda saura suka yi domin tattaunawar tana kara fahimtar aiki.
Ina son a gaba a kiyaye da wannan a hada alkalai wuri daya.
An yi wannan aikin an kare, ko kin hadu da wani kalubale?
Gaskiya in ka cire kalubalen lokaci ban hadu da wani abu ba, domin a sa’ar da aka ba da aikin akwai wasu ayyuka a makaranta.
Kina ganin gasa na iya kara bunkasa marubuta a kafofin watsa labarai musamman jaridu da gidajen rediyo?
Da za a san yadda Adabin Hausa ya fara a 1927, kila sama da shekara 100, tun sannan ake shirya gasar harsunan Afirka kuma Hausa na shiga a lokacin, haka har zuwa 1930 da 1933 inda aka samar da littattafai irin su Takobin Gaskiya da Magana Jari Ce da Ruwan Bagaja.
Har yanzu masu nazarin Harshen Hausa littattafan ne suke cewa sun fi inganci. Dawo da gasa ana son a inganta Adabin Hausa ke nan.
Kina ganin baiwar rubutu da waka suna iya zama daya a kuma same su ga mutum a lokaci guda?
Ana iya samun fuska uku, akwai wanda yake baiwarsa ta kirkirar labari ce kawai, akwai wanda yana iya waka ya rubuta ya rera, ko kuma ya rubuta kawai, za ka ga wani wasan kwaikwayo yake iya rubutawa.
Kina ganin jigon da marubuta suke dauka ya yi daidai da wannan zamani?
Eh, kamar wannan da Aminiya ta dauka a kan siyasa, ka ga tana ci yanzu, kusan komai ita take tafiyar da al’umma.
In aka dauki jigon siyasa ina ganin an yi daidai domin ita take tafiyar da rayuwa.
Kila bayan wannan ana iya tafiyar da wani jigo daban kamar tattalin arziki, amma dai har yanzu akwai bukatar sake daukar jigon siyasa domin sake bankado wasu abubuwa masu yawa da suka shafi siyasa don a san su da kyau.
Wane fata kike da shi ga wadanda suka yi nasara a gasar ta Aminiya?
Ina so su ci gaba da zama marubuta, kuma su rika daukar abubuwan da suke faruwa cikin al’umma suna rubutu a kansu. Domin adabi hanya ce ta inganta tunanin al’umma.