Bambancin sha’awa a tsakanin ma’aurata (4)
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar da bambancin sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin. […]
Assalamu Alaikum. Barkanmu da sake haduwa cikin wannan fili. Ga ci gaban bayani a kan abubuwan da ma’aurata za su aikata don tafiyar da bambancin sha’awa a tsakaninsu, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga duk masu bukatarsa, ya kuma haifar da karuwar farin ciki da jin dadi cikin rayuwar aurensu, amin.
Abu na 3: Ma’aurata su tuna cewa, da zarar igiyar auren nan ta kullu tsakaninsu, to shi ke nan sun zama daya a ruhi da jiki, ta kowace fuska da kuma kowane bangare na rayuwarsu, dole farin cikin daya ya shafi daya. An san cewa 1 a tara da 1 amsar 2 ce, to amma ban da cikin rayuwar aure, a rayuwar aure dole kodayaushe ya kasance 1+1=1, don haka ko me daya daga cikin ma’aurata zai yi, to dole ya yi tunanin tasirin abin nan ga dan uwan shi da rayuwar aurensu. Bai kamata ba ga daga daga cikin ma’aurata ya so kan shi shi kadai, dole sai dai ya so kan shi tare da dan uwan aurensa, bai kamata ba daya na cikin dadi da kwanciyar hankali amma dayan na cikin kunci. Wani lokacin sai ka tarar ma’aurata suna nuna halin ko in kula ga halin da ‘yan uwan aurensu ke ciki, ko kuma su ma dage wajen ganin sun kuntata wa juna. Wajibi ne ga ma’aurata da suke son nasara duniya da lahira cikin rayuwar aurensu su cire son rai, su guji cutar da juna su kasance masu kula da halin da dayan suke ciki, su kuma kasance masu gaggawar yin abubuwan dadadawa juna rai, da fatan Allah Ya ba mu ikon dagewa a kan duk wani abu na kwarai, amin.
Abu na 4: Ma’aurata ku tuna cewa sunan ku ba miji da mata kadai ne ba, ko maigida da uwargida, ko Alhaji da Hajiya, ko baba da Mama, babban sunanku, wanda ya fi kowanne fa’ida shi ne kasancewar ku Masoyi da Masoyiya! Da zarar an yi aure, yawanci sai a watsar da ‘yan kalaman soyayyar nan masu dadi da dadadawa, a biye wa al’ada, wasu ma’auratan ma sai su gama rayuwar aurensu ba tare da furta kalaman soyayya da yin abubuwan nuna soyayya ga junan su ba! Duk Maigidan da yace da Uwargidan sa: “Wallahi Ina bala’in son ki” dadin da zata ji ba ya misaltuwa, wannan sai yafi motso da sha’awar sama da wani wasan ibadar aure, mata su na tsananin son jin irin wadannan kalaman daga wajen mazajensu, kuma rashin ire-iren su shi ke dakusar da sha’awar mafi yawa daga cikin matan aure. Wannan wani abu ne da baya isar kowace diya mace musamman daga wajen mijin da ta ke aure.
Abu na 5: Abu na 5 da yawanci ma’aurata kan mance da shi cikin rayuwar aurensu, shine sadaukarwa, wannan wani babban jigo ne na rayuwar aure kuma ajiye shi gefe da yawancin ma’aurata ke yi shi ke kawo matsaloli cikin rayuwar aurensu. Babban abinda ke kawo rashin sadaukarwa cikin rayuwar aure shine karanci ko rashin soyayya, domin in kana son abu dole ka sadaukar da rayuwar ka gare shi, don haka Uwargida, in dai kina son Maigidanki kina kaunarsa, to sai ki sadaukar da lokacinki, karfinki, da jin dadinki don faranta masa, haka ma Maigida!
Hanya Ta 4: Sa Ranar Ibadar Aure:
Wannan hanya tana da matukar alfanu wajen daidaita duk wani raunin ibadar aure da ke tsakanin ma’aurata. Sai ma’aurata su tsaida wata rana ta musamman don ibadar aure, sanin cewa akwai wannan muhimmiyar ranar, kwakwalwar su za ta zama cikin shirin isowar ta, kuma za ta tanadar masu duk abubuwan da suka kamata don ganin an cimma burin wannan ibadar auren. Sannan su kan su ma’auratan za su zama cikin shiri na kai da na zuciya don tarbar wannan rana da wannan muhimmiyar ibadar.
Ma’aurata suna da zabin su bar wannan rana ita ce kadai ranar aiwatar da ibadar aurensu haka kuma suna da zabin su rika aiwatarwa duk lokacin da suka so amma duk da haka su fitar da wata ranar ta musamman da za ayi soyayyyar ibadar aure ta musamman a cikinta, wacce za a tanadar ma dukkannin abin tanadi don samun nasararta. Kowanne daga cikin ma’aurata ya kure wajen shiri duka na kai da na zuciya.
Kuma wannan rana a sa mata wata ajanda ta musamman, misali ga ma’auratan da Uwargidan ke da matsalar karanci ko rashin cimma biyan bukatar sha’awa, sai su sa wannan ne ajandarsu a ranar, wani kewayowar kuma su sa wata ajandar daidai da irin bukatun ma’aurata.
Sai sati na gaba Insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a kodayaushe, amin.