Bambancin Yaren kaunar Ma’aurata
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili, fatana Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A ci gaba da bayanin da muke kawo muku kan sinadaran da ke haifar da sarkewar soyayyar ma’aurata, a yau in sha Allah za mu tattauna […]
Assalamu Alaykum wa rahmatullahi wa barakatuh. Ina mana marhabin da sake haduwa cikin wannan fili, fatana Allah Ya amfanar da mu dukkan bayanan da za su zo cikinsa, amin. A ci gaba da bayanin da muke kawo muku kan sinadaran da ke haifar da sarkewar soyayyar ma’aurata, a yau in sha Allah za mu tattauna kan yadda rashin fahimtar yaren soyayyar juna ke haifar da sarkewar soyayya tsakanin ma’aurata, da fatan Allah Ya sa wannan bayani ya isa ga masu bukatarsa kuma ya amfanar da su, amin.
Ma’ana
Yaren kauna: Na nufin abubuwan so da kauna da ake aikatawa ko aiwatarwa ga wanda ake so da nufin bayyanar da so da kaunar da ake masa a cikin zuciya. Soyayya irin ta tsakanin ma’aurata tana da yarurruka guda hudu: Kalaman kauna; Kyauta da kyautatawa; Shafar kauna da kuma Ayyukan sadaukarwa. Idan muka lura kusan kowanne daga cikin ma’aurata na bukatar wadannan yarurruka hudun nan daga wajen wanda yake aure, amma sai dai kowanne akwai wani yare da ya fi ba muhimmanci sama da sauran, wanda idan ya kasance wanda yake aure bai yi masa shi ba, to zuciyarsa ba za ta samu natsuwa ba, za ta yi ta kokwanto game da tabbatuwar wannan so da kaunar.
Tasirin Yarukan kauna Cikin Soyayyar Ma’aurata
Kamar yadda ‘yan Adam suka bambanta a siffofi da halayensu, to haka kuma suka bambanta a bukatun soyayyarsu, kowanne ya bambanta da dan uwansa ta fannin abubuwan da yake so a yi masa wajen bayyana so da kauna gare shi. Wadannan yaruka na soyayya suna da matukar tasiri cikin soyayyar ma’aurata, ma’auratan da suka dace yarensu ya zamo iri daya ne, to wannan zai kara karko da dankon soyayyar da ke tsakaninsu. Amma idan ya kasance an samu bambanci, to wannan zai haifar da sarkewar soyayya tsakaninsu, zai sa ma’aurata su yi ta zaman doya da manja, kowa na zargin kowa a kan rashin nuna damuwa da kulawa.
Bambancin yaren kauna shi ne- rashin fahimtar juna tsakanin ma’aurata dangane da yanayin bayyana soyayya da kuma samun bambanci cikin abubuwa masu dangantaka da soyayya da kowannensu ya fi ba muhimmanci. Kowanne dan Adam yaren soyayyarsa daban da na dan uwansa, wanda idan ba da wannan yaren aka nuna masa soyayya ba, to ba zai fahimci cewa ana son sa ba. Misali:
“Halayen maigidana sun ishe ni, gab nake da in bar gidansa! Domin baya ganin girman mahaifana da ‘yan uwana gaba daya, kuma sai ya rika ikirarin shi mai kaunata ne, mai nuna soyayya gare ni!”
Daga bayanin wannan baiwar Allah, muna iya fahimtar cewa, mutunta mahaifa da ‘yan uwanta shi ne yaren soyayyar da take bukata daga wajen mijinta, shi ya sa duk kulawar da zai ba ta, duk nuna kaunar da zai mata, ba zai faranta mata rai ta ji dadi ba kamar a ce idan yana mutunta mahaifa da ‘yan uwanta.
Yadda Ma’aurata Za su Fahimci Yaren kaunar Junansu:
Ma’auratan da suka fahimci cewa ba su samun irin yanayin bayyanar da soyayyar da suke so, ko wadanda suka fahimci cewa suna ta hidimomin bayyana soyayya ga wadanda suke aure, amma su din ba su nuna jin dadinsu, to sai su bi wadannan hanyoyin wajen warware wannan sarkewa.
• Ta hanyar sanar da juna kai tsaye cewa: “Ni fa kaza da kaza ne na fi so, su ne abubuwan da suke burge ni kuma su ke sa in ji dadi cikin zuciyata; kuma kaza da kaza ba su burge ni ko ba su dame ni ba.
• Tambaya kai tsaye ga abokin auren da ake yi wa hidimomin nuna so da kauna, amma ba ya nuna alamun ya ji dadinsu ba: “Na ga idan na yi kaza da kaza da niyyar bayyanar da soyayyata gare ka ba ka nuna jin dadinka game da abin da na yi; to don Allah ina son ka sanar da ni kaza da kazan da kake so in rika yi maka, da kuma kaza da kazan da ba ka so don in guje su?” Ko wata hanya makamanciyar wannan.
• Ko ma’aurata su dage wajen gano yaren soyayyar junansu daga cikin yarukan nan guda 4? Ta hanyar lura da wadanne irin abubuwan ne idan aka yi su suke matukar nuna jin dadi da murnarsu dominsa? To sai a lakanci abin nan a rika yawan aikata shi. Idan kuma akwai wani abu da ake yawan yi don nuna soyayya amma wanda ake yi dominsa ba ya nuna jin dadinsa ba, to sai a daina yinsa na wani lokaci, in har aka ji bai tanka game da hakan ba, to lallai bai ba wannan abin muhimmanci ba a matsayin makamin nuna soyayya gare shi, idan kuwa ya tanka din sai a tamabaya ashe yana son kazan nan? Amsar da ya bayar ita za ta sa a fahimci muhimmancin abin a gare shi.
• Haka kuma ma’aurata na iya rubutawa a takarda dukkannin abubuwan da suke so a rika yi musu wadanda yake sa su jin dadi da farin ciki da kuma abubuwan da ba su so da kuma abubuwan da ba su dame su ba. Ko su aika da sakon tes a wayarsu, ko ta hanyar wayo da dabara da zaurance, ta yadda wanda ake aure idan ya ji, ya gani ko ya karanta zai fahimta kuma ya yi kokarin gyarawa ba ta hanyar zargi da mita ba, wannan sai dai ma ya sa ma’auraci ya kara janye jikinsa daga aikata abubuwan da ake bukata din.
• Wata muhimmiyar hanyar da ma’aurata za su fahimci yaren kaunar junansu shi ne ta hanyar lura da abubuwan da wanda suke aure yake yawan yi don nuna kaunarsa gare su, domin abin nan da suke yawan yi, to su a wajen su shi ne iyakar soyayyarsu, don haka irin yadda suke yi din nan, idan aka yi musu shi zai sa su ji matukar dadi cikin zuciyarsu; misali:
“Na karanta bayaninki na hanyoyin kayatar da maigida ranar sallah, na kuma aikata hakan amma Maigidana bai nuna mini jin dadin abin da na yi ba, ya ma goge duk wani sakon nuna kaunar da na aika masa a wayarsa.”
Daga bayanin wannan baiwar Allah za mu iya fahimtar cewa dadadan kalamai su ne yaren soyayyarta, don haka su ta yi wa mijinta, shi ya sa ba ta ji dadin goge su din da ya yi ba. Rashin nuna jin dadin maigidanta zai sa ta ga kamar kila bai damu da ita ba? Ta yiwu bai fahimci muhimmanci abin da ta yi masa ba shi ya sa, ko kuma shi ma bai fahimci nata yaren kaunar ba. Sannan hakan kuma ya nuna wadannan hidimomi da ta yi masa ba su ne yaren kaunarsa ba. Inda ta tambaye shi, sai ta yi mamakin jin cewa wani abu ne mai saukin aikatawa, ko inda ta lura da kyau za ta iya fahimtar yaren kaunarsa da kanta wadanda idan ta aikata su za ta ga tasiri mai kyawu.
Sai sati na gaba in sha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarsa a kodayaushe, amin.