Bambaron Baro da Cuku-cukun Cunkuncu

’Yebe Iya debe Ki kwashe kayan bebe Bar ni da watsattsaken zube Batutuwa duk nai musu zobe   A mayar da wuka kobe Fadan a bari sai gobe Managartan ayyuka a zuzzube Masu hankali a yi dube-dube Kar a fara dambe   Kwamacala a kebe Hatsaniya ta cabe Minista da ma’aikata an babe Baba sai […]

Bambaron Baro da Cuku-cukun Cunkuncu

’Yebe

Iya debe

Ki kwashe kayan bebe

Bar ni da watsattsaken zube

Batutuwa duk nai musu zobe

 

A mayar da wuka kobe

Fadan a bari sai gobe

Managartan ayyuka a zuzzube

Masu hankali a yi dube-dube

Kar a fara dambe

 

Kwamacala a kebe

Hatsaniya ta cabe

Minista da ma’aikata an babe

Baba sai ka yi dabe

Ko a daina daga lebe

 

Kwantiragin cuku-cuku

Kamun kazar kuku

Tunkuzar tunku

Tabargazar duku-duku

Kwarmaton iya taku

 

Lamarin ga akwai shakku

Haya-haya kamar a doku

Da muku-muku

Aka ce wani ya maku

Turak-turkar turakar turaku

 

Watsattsaken waskiya

Wasika ga Baban-burin-huriyya

Salwantar Hauro tiren-taliya

An kisma yawan kasan manuniya

Wai Mai shago ya juya

 

Azargagiyar zargi

Zarge-zarge da kugi

Tsallen takun agwagi

Mai kwakwazo na magagi

An kashe bakin mai gigi

 

Ka ce an yi kwantiragi

Tiren-taliya babu ragi

Rashin biyayya babu waigi

An sagaleka a sagagi

Sai kake ta bambamin rugugi

 

Ministan tunkuza

Ka yi taga-taga ka gaza

Sai ka mike ka tagaza

Mai shago ya dauki batunka banza

kazafinka ko’ina an baza

 

Bambaro 

Bararo mai baro

Almarar Allanguburo

Fullo ya iya sharo

Bobo da kwambo sai mai biro

 

Cuku-cuku

Casu sai cunkuncu

Cuna ta kama wuta cuu

Camamar cin cuku

Caccakar caku

 

Babbaku da farfaru

Burgar bunsuru

Take-taken takun zuru

An fara dabarbaru

Tunkuzar tashin tantabaru

 

Fandararru

Fetsararru

kangararru

kadangaru

Masu fasa mana garu

 

kiren karairayi

karya mai kaikayi

kayar kayoyi

korafin kiyayyar sauyi

karajin kulafucin son matsayi

 

Haurobiyawa  masu ka-ce-na-ce

Baba zai fayyace

Zancen zaure ne zaurance

Kwanakin ga nai kwatance

Kar a bar al’amura su kazance

 

Tsarin tsayuwa

Tsaba da tsakuwa

Tsibi-tsibin totuwa

Tsokacin tsoho da tsohuwa

Tsatsubar tsomomuwa

 

Mu ci tuwo da miyar yakuwa

Ina Haurobiyawa

Muna muku yekuwa

Mu kara karar amsa kuwwa

A hada kai a kiyayi kokowa

 

Lallai mu fatattaki ’yan wawa

Masu yi mana tsiwa

Sai na daka musu tsawa

Bisashe a ci harawa

Makekiyar makiyaya ce a dawa

 

Dabbobi na cin ciyawa

Garka da gayauna

Hatsi ya zo an amfana

Adawa in babu dawa

Wasu za su shiga dawa

 

Baba ya hana kwashi-kwaraf

Ballantana ai wa lalita karkaf

Wani na kukan an kife shi kif

Har ya dauke wuta dif

Ya shirya gidoga tsaf

 

Haurobiyawa Cuku-cukun Cunkuncu da Dabarbarun bambaron Baro da ke takun saka a Kamfanin tunkudo tunkuzar Haurobiya ya dauki hankalin jaridu da mujallun kasar, inda ake ta ka-ce-na-ce, har ma an karke da watsattsaken wasika da aka rika baza wa duniya. Baban-birin-huriyya dai ya fasko bsatun ingarman karfen karafa, watakila ma shi ya sa ya tsuke bakinsa, tunda an ce shi ya rattaba hannu kan amincewa da kwantiragin da ake kokarin kwantara wa Mai tantabaru kwagiri saboda shi.

Kullum dai a farfajiyar wannan makaranta mun sha fadi a bi doka don ka da a koka; a bi ka’ida sai a samu fa’ida, a bar mu mu sarara ko ma samu sa’ida. Don haka nike ganin da Ministan tunkuza bai shiga cuku-cukun Cunkunci ba, ai da bai yi karon-batta da Dabarbarun bambaron Baro, har suka cusa al’umma cikin rudani da tsoro.

Cuku-cukun Cunkuncu da Dabarbarun bambaron Baro ba mafita ba ce, musamman daidai wannan lokaci da ake fama da karyewar darajar albarkatun man tunkuza a kasuwannin duniya. Mu yi yunkurin karkata akalar albarkatun kasarmu kan labin kowace hanyar samu, domin kada mu damu, illa dai akai-akai mui rika samun damu, har ma mu karke da gasa damin tumu, amma a rage wa ’yan dugwi-dugwi tarin geron da za a sarrafa a rika a hada musu kamu. kin aiwatar da managartan dabaru da warware dabaibayin cuku-cukun cunkuncu na iya jefa kasar nan cikin turun kamammanmu.

Batu na ingarman karfen karafan kwangirin titin tarragon layin dogo, lokaci ya yi da Baban-burin-huriyya zai kafa doka cewa duk wanda ya yi wa gwamnati tonon silili kuma ta tabbata shi ne a kan doron bata, to za a tabbatar da cewa mukaminsa ya yi batan-baka-tantan.

Baba ka ja musu na zomo, ka zuba musu na-mujiya, ka kuma yi kokarin shawo kan duk wata hatsaniya, don gudun kada a karke da bahallatsa, har a shiga nunin yatsa, ko a kutsa uwar daka a kitsa miyagun al’amuran da zai hargitsa tattalin dukiyar kasa ya yi watsa-watsa. A mafi yawan lokuta ina gaya maka Baba ‘tsaya tsaf ka kimtsa.’ Kada ka yarda da ZUkI-TA-MALLE kama kare ka hada shi da zomo. Nauyi ne dai al’umma ta dora maka sai ka kara shirin nada gammo.

Lallai mu kasance masu kyakkyawar aniya, mu kiyayi waskiya da son rai a fafutikar neman mukami, har mu mutsuttsuke mukamuki ko laifinmu ya sanya a cafke mu a kundukuki.