Bamu taimakawa Nnamdi Kanu tserewa ba- DSS

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta musanta zargin da ake yi wa jami’an hukumar biyar akan tserewar jagoran ‘yan awaren Biyafara na kudu maso yammacin Najeriya Nnamdi Kanu daga masaukinsa a Umuahia babban birnin jihar Abiya zuwa kasar waje. Nnamdi Kanu ya fice daga kasar ne tun a watan Satumba shekarar 2017. Kakakin hukumar DSS […]

Bamu taimakawa Nnamdi Kanu tserewa ba- DSS

Hukumar tsaron farin kaya (DSS) ta musanta zargin da ake yi wa jami’an hukumar biyar akan tserewar jagoran ‘yan awaren Biyafara na kudu maso yammacin Najeriya Nnamdi Kanu daga masaukinsa a Umuahia babban birnin jihar Abiya zuwa kasar waje.

Nnamdi Kanu ya fice daga kasar ne tun a watan Satumba shekarar 2017.

Kakakin hukumar DSS Peter Afunanya ne ya bayyana wa manema labarai hakan jiya Litinin.