Ban amince da hana masu korafi zuwa kotu ba – Buhari
Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya nuna rashin amincewa da matakin da jam’iyyarsa ta APC ta dauka na hana ’ya’yanta da aka kuntata musu zuwa kotu, tare da yin barazanar ladabtar da su, inda ya ce bai kamata a hana ’ya’yan APC damar gurfanar da ita a gaban kotu ba, domin neman hakkinsu sakamakon rashin adalcin […]
Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ya nuna rashin amincewa da matakin da jam’iyyarsa ta APC ta dauka na hana ’ya’yanta da aka kuntata musu zuwa kotu, tare da yin barazanar ladabtar da su, inda ya ce bai kamata a hana ’ya’yan APC damar gurfanar da ita a gaban kotu ba, domin neman hakkinsu sakamakon rashin adalcin da suka yi zargin an yi musu a zabubbukan fid-da-gwani na jam’iyyar kwanakin baya.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Litinin da ta gabata. Yana mai cewa, “Ban amince da matsayin jam’iyyarmu ba da ta haramta wa mambobin da aka bata wa rai zuwa kotu, inda take gargadin ladabtar da su.”
Ba zai yiwu da gangan mu tauye hakkin mutane ba. Mun amince mu gudanar da zaben fid-da-gwani ta hanyar ’yar-tinke ko hanyar wakilai ko kuma yin sulhu tsakanin masu son yin takara, sannan muka amince cewa duk wanda ya ga ba a yi masa adalci ba zai iya zuwa kotu.Ya kamata kotu ta kasance wuri na karshe da mutanen da ba su gamsu ba, za su nufa. Don haka ba zan amince da yanayin da jam’iyya za ta hana wani zuwa kotu ba,” inji Shugaba Buhari. Sai dai Shugaban ya ce zai fi son a magance matsalar ba tare da an je kotu ba.
Masu ruwa-da-tsaki a jam’iyyar, ciki har da Uwargidan Shugaban Kasa, A’isha Buhari, sun soki APC bisa rashin adalcin da suka ce ta yi ga masu neman takara.
A’isha Buhari ta ce “Abin takaici ne a ce wadansu ’yan takara su yi amfani da kudin guminsu su sayi fom na takara, sannan an tantance su, kana sun yi yakin neman zabe iya karfinsu, amma kuma a cire sunayensu a ranar zabe.”
Ta zargi Shugaban Jam’iyyar Adams Oshiomhole, wanda ta ce sananne wajen kokarin kwato wa talakawa ’yancinsu, sannan a ce ya kitsa rashin adalci a APC. Zargin da ya musanta.
Wadansu gwamnonin APC irin su Abdul’aziz Yari na Zamfara da Ibekunle Amosun na Ogun da Rochas Okorocha na Imo, sun sha sukar shugaban jam’iyyar game da yadda ya gudanar da zabubbukan fitar da gwanin na APC.
Rikicin da ya kaure a tsakanin ’yan takara a Jihar Zamfara ya yi sanadin gaza mika sunayen ’yan takarar Gwamna da Majalisar Dokoki ga hukumar zabe har wa’adin mika sunayen ya kare.