Ban bi mahaifina zuwa PDP ba – Babbar ‘Yar Atiku
Babbar ’yar gidan tsohon Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, Fatima Abubakar ta bayyana cewa ba ta bi mahaifinta canja sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP ba. Fatima Atiku Abubakar, wadda ita ce Kwamishinar Lafiya ta Jihar Adamawa, a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana wa jaridar yanar gizo ta Premium Times cewa a halin […]

Babbar ’yar gidan tsohon Shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, Fatima Abubakar ta bayyana cewa ba ta bi mahaifinta canja sheka daga Jam’iyyar APC zuwa PDP ba.
Fatima Atiku Abubakar, wadda ita ce Kwamishinar Lafiya ta Jihar Adamawa, a ranar Larabar da ta gabata ta bayyana wa jaridar yanar gizo ta Premium Times cewa a halin yanzu al’amurran ayyukan da ta sa a gaba su ne a gabanta, ba maganar canza sheka da mahaifin ta ya yi ba.
Kwamishinar ta yi wannan jawabi ne kwana daya bayan jaridar The Sun ta ruwaito cewa ta ajiye mukaminta na kwamishina a Jihar Adamawa karkashin gwamnatin APC, ta bi mahaifinta Atiku zuwa PDP.
Fatima Atiku Abubakar mai shekaru 45, ita ce babbar ’ya ga Alhaji Atiku, Wacce Gwamnan Jihar Adamawa, Sanata Muhammed Jibrilla Bindow ya nada ta kwamishinanar harkokin lafiya ta jihar a shekarar 2015.
Idan za a iya tunawa, a lokacin da aka nada ta kwamishina, ta bayyana cewa ba ta bukatar albashi ko alawus ko na sisin kwabo, tana mai cewa, ta je ne don ta yi wa jihar ta ta haihuwa hidima domin kishin jihar da kuma kishin kasa.
An buga labari a jaridar The Sun ta ranar Talatar da ta gabata cewa Fatima, tare da wasu kwamishinoni takwas sun sauka daga gwamnatin Gwamna Bindow sun bi Atiku zuwa PDP. Baya ga Fatima da ta karyata labarin ficewa daga daga APC, haka shi ma Kwamishinan Filaye da Safiyo na Jihar Adamawa, Yayaji Mijinyawa ya musanta batun ficewa daga jam’iyyar ta APC, inda y ace yana nan daram.
A ranar Lahadin da ta gabata ne Alhaji Atiku Abubakar ya aiyana komawarsa PDP a karo na uku tun sa’ar da ya fice daga jam’iyyar a shekarar 2007, bayan da ya shafe shekaru takwas a matsayin mataimakin shugaban kasa.