Ban ci bashin N10bn na CCTV ba – Ganduje

Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta zargin  cin bashin N10 biliyan domin saka kyamarorin tsaro na CCTV a Birnin Kano da kewaye. Wani gungun ƴan gwagwarmaya ƙarƙashin inuwar Coalition of Political Analysts Forum and Good Governane ya nemi gwamantin Abba Kabir Yusuf ta bincike tsohon gwamna bisa abin da ya yi […]

Ban ci bashin N10bn na CCTV ba – Ganduje

Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje

Tsohon Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya musanta zargin  cin bashin N10 biliyan domin saka kyamarorin tsaro na CCTV a Birnin Kano da kewaye.

Wani gungun ƴan gwagwarmaya ƙarƙashin inuwar Coalition of Political Analysts Forum and Good Governane ya nemi gwamantin Abba Kabir Yusuf ta bincike tsohon gwamna bisa abin da ya yi da kuɗin.

Sai dai a martanin da ya fitar a Abuja, Dr Ganduje ya bai samu zarafin karɓo bashin ba saboda wata Kotun Tarayya dake Kano ta dakatar da shi bayan da Majalisar Dokoki ta amince masa.

Kotu ta bai wa Gwamnatin Kano umarnin sakin Kwamishinan Ganduje

Kotu ta dakatar da sammacin Ganduje kan bidiyon dala

A sanarwar da kwamishinan yaɗa labarai na gwamnatin Ganduje, Malam Muhammad Garba ya sa hannu, tsohon gwamnna ya ƙalubalanci gungun ƴan gwagwarmayar da su kawo hujjar cewa ya karɓo bashin.

Dr Ganduje ya kuma yi zargin cewa gungun ƙungiyoyin na boge ne waɗanda iyayen gidansu na siyasa ke ɗaukar nauyinsu domin ɓata masa suna.