Ban debe tsammanin Arsenal za ta lashe Firimiyar bana ba —Arteta

Arteta ya ce bai ji dadin rashin nasarar da ya yi a hannun Manchester City ba.

Ban debe tsammanin Arsenal za ta lashe Firimiyar bana ba —Arteta

Kociyan Arsenal, Mikel Arteta, ya ce har yanzu bai fidda rai kungiyar za ta lashe Firimiyar Ingila ta bana ba. 

Arteta ya yi wannan furuci ne duk da shan kayen da Arsenal ta yi a hannun Manchester City da ci uku da daya a fafatawarsu ta ranar Laraba.

Kociyan ya ce duk da bai ji dadin rashin nasarar ba, amma hakan bai sanya shi karayar cewa za su rasa damar dage kofin Firimiyar a bana ba.

Arteta shi ne dai tsohon mataimakin kociya a Manchester City gabanin karbar ragamar horar da Arsenal.

A yayin zantawarsa da manema labarai bayan wasan na jiya, ya ce kayen ne ma ya kara mishi kwarin gwiwar cewa za su iya lashe kofin na bana.

Bayan doke Manchester United a ranar 22 ga watan nan, Arsenal na jagorancin teburin na Firimiya ne da tazarar maki 5 baya ga kwantan wasa guda a hannu.

Sai dai daga wancan lokaci zuwa yanzu, maki daya kacal ta iya samu daga maki 9 wanda sauran suka zille mata.

Sai dai duk da hakan, Arteta ya ce gabanin wasan na jiya yana da shakku amma bayan ganin yadda ta kaya ne ya samu yakinin cewa tabbasa Arsenal za ta iya lashe gasar.

Da rashin nasarar ta jiya dai ya nuna yadda Guardiola ya yi nasara a wasanni 8 cikin 9 da ya jagoranta zuwa Arsenal karkashin Mikel Arteta.