Ban ga dalilin ta da jijiyar wuya don mun gayyaci Zakir Naik ba —Sarkin Musulmi

Sakin Musulman ya ce Musulmai na da ’yancij gayyatar duk dan uwansu da suka ga dama

Ban ga dalilin ta da jijiyar wuya don mun gayyaci Zakir Naik ba —Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya ce Musulman Najeriya na da ’yancin gayyatar dan uwansu daga ko’ina a fadin duniya domin ya yi wa’azi a kasar.

Basaraken na mayar da martani ne ga masu sukar lamirinsa kan gayyato fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mai wa’azi dan asalin kasar Indiya, Sheikh Zakir Naik.

Malamin ya isa Sakkwato ne a farkon makon nan domin yin wa’azi a wasu jihohin Najeriya, bisa gayyatar Sarkin Musulmin.

To sai dai da yake mayar da martani ga masu sukar lamirin nasa yayin rufe taron Makon Usmanu Danfodiyo da ya gudana a Sakkwato, Sarkin Musulmi ya ce, “Shi Musulunci daya ne duk inda ka je.

“A matsayinmu na Musulmai, muna da damar gayyatar ’yan uwanmu Musulmai domin yin mu’amala da su. Na fara haduwa da Dokta Zakir Naik tun shekaru 11 da suka gabata.

“Sakkwato na farin cikin karbar bakuncinka. Mu muna alfahari da kasancewarmu Musulmai, kuma muna aiki ne domin cigaban Musulunci, ba wai kowa ba.

“Mu Musulmi ne saboda haka Allah Ya ga dama, kuma babu wanda ya isa ya canza haka, muna gode wa Allah da Ya yi mu a matsayin Musulmai,” kamar yadda ya bayyana yayin gangamin rufe taron a Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa da ke Sakkwato.

Sarkin Musulmin ya ce malamin ya yi kokari matuka wajen ilimantar da Musulmi da ma wadanda ba Musulmi ba abin da Musulunci ya kunsa.

Shi ma da yake jawabi a wajen taron, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mahmud Yayale Ahmed, ya jaddada ci gaba da bayar da goyon baya na miliyoyin Musulman kasar nan ga Sarkin Musulman.