Ban gajiya ga ‘yan Najeriy

Zan yi amfani da wannan dama in yi bangajiya ga ’yan uwa ’yan Najeriya musamman ga wadanda suka jefa kuri’arsu ga ’yan takarar da suke so a zaben da ya gudana makon da ya wuce wato zaben shugaban kasa da ’yan majalisar Dattawa da na na ’yan majalisar Wakilai. Tabbas ’yan uwana ’yan Najeriya sun […]

Ban gajiya ga ‘yan Najeriy
Ban gajiya ga ‘yan Najeriy

Zan yi amfani da wannan dama in yi bangajiya ga ’yan uwa ’yan Najeriya musamman ga wadanda suka jefa kuri’arsu ga ’yan takarar da suke so a zaben da ya gudana makon da ya wuce wato zaben shugaban kasa da ’yan majalisar Dattawa da na na ’yan majalisar Wakilai. Tabbas ’yan uwana ’yan Najeriya sun kafa babban tarihi kuma sun yi abin burgewa da yabo gami da koyi da su.Kowa ya san yadda aka rika gudanar da zabuka a

Najeriya tun daga shekarar 1999/2003/ 2007/2011,cikin kwama cala da kazanta .Wadancan zabuka ’yan Najeriya da kansu sun yi Allah wadai da yadda aka gudanar da su.Hatta kasashen waje su ma sun yi Allah wadai da yadda aka gudanar da wadancan zabuka. Musamman idan aka yi la’akari da yadda ake kallon Najeriya a matsayin giwar Afirika ko in ce su yaya babba wadda ya kamata a ce ta tsare kanta daga aikata duk wasu abubuwan da za su iya zubar mata da mutunci.Sannan ta rika yin kyawawan abubuwa wandanda wasu za su rika koyi da ita.Akwai wata magana da masu iya magana suke cewa” Mahakurci mawadaci”.Ko kuma komai zafi wata rana sanyi zai zo”.’
’Yan uwana ’yan Najeriya sun gudanar da zubuka a makon da ya shude sai dai wannan zabe ya zo wa dimbin jama’a da ba zata. Ganin yadda Najeriyar take gudanar da zabuka masu muni sosai wanda kuma a duk zabukan idan za a yi su sai an samu salwantar dimbin rayukan jama’a, yayin da wasu kuma ake mai da su nakasassu.To sai dai a wannan karon, rawar ta canza sosai domin an gudanar da zabukan ne cikin kwanciyar hankali da lumana duk da dai akwai ’yan wasu matsaloli kadan da wasu suka fuskanta nan da can.To amma duk da hakan wannan zabe an yi shi ne cikin tsafta.Wanda kuma idan har za a dore a haka, to Najeriyar da duniya take kyama,za ta zamo abin kauna, abin so, abin koyi ga wasu.Wannan zabe dimbin ’yan Najeriya sun hada kawunansu a wuri daya domin ganin sun tsaftace kasarsu daga kazantar da wasu gurbatattun shugabanni suka goga wa kasar.Amma ’yan Najeriyar sun samu nasarar kama hanyar tsaftace zabensu ne tare da tallafi ko samun kwarin gwiwa daga hukumar zabe ta INEC karkashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega. Ta hanyar yin amfani da na’urar tantance masu jefa kuri’a wato Card Reader. Hakika wannan na’ura ta taimaka sosai wajen rage aringizon kur’u ko in ce magudin zabe.’Yan Najeriya sun gudanar da zabe salin alin,abin gwanin burgewa wanda dimbin jama’a na cikin gida da na waje suka yaba da yadda aka gudanar da zaben.Saboda haka nake yi wa ’yan uwa ’yan Najeriya bangajiya bisa ga wannan kokari da suka yi.
Da fatan yadda suka gudanar da wannan zabe lafiya, ina yi mana fatan mu yi wanda ya fi shi kyau da tsafta a zaben gwamnoni da na ’yan majalisun jihohi da za a yi nan da ’yan kwanaki kadan da fatan za mu yi shi lafiya mu gama lafiya. Da fatan su kuma shugaban nin da muka zaba da wadanda za mu zaba nan gaba za su gaggauta share mana hawaye su kuma cire mana kitse daga wuta domin inganta rayuwarmu da ta dade a cikin kunci.

Haruna Muhammad Katsina.
Shugaban kungiyar Muryar Jama’a ta Jihar
Katsina.
07039205659 ko 07057491050
[email protected]