Ban gamsu da hukuncin kotu kan zaben Bauchi ba, zan ɗaukaka ƙara – Sadique
Ya ce tuni ya umarci lauyoyinsa su daukaka ƙara
Dan takarar Gwamnan Jihar Bauchi na jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata, Sadique Abubakar, ya ce bai gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe ba na korar kararsa.
Sadique, wanda tsohon Babban Hafsan Sojojin Sama na Najeriya ne, ya ce tuni ya umarci lauyoyinsa da su ɗaukaka ƙara.
- Gobara a wajen ajiye man fetur ta kashe mutum 35 a Kwatano
- Jami’ar Maiduguri za ta kafa gidan tarihin tunawa da rikicin Boko Haram
Ya ce zai bi dukkan matakan da doka ta tanada don ganin ya kwato abin da ya kira “hakkinsa” wanda ya ce mutanen Jihar sun ba shi a yayin zaɓe.
“Muna da ƙwarin gwiwa kan tarin hujjojin da muka gabatar, cewa kotun gaba za ta yi la’akari da su. Insha Allahu za mu kwato haƙƙinmu da aka yi mana fashinsa,” in ji Sadique.
A ranar Larabar da ta gabata ce dai kotun sauraron kararrakin zaben Gwamnan Jihar ta yi watsi da ƙarar dan takarar inda ta tabbatar da nasarar da Bala Mohammed na PDP ya samu a zaɓen ranar 18 ga watan Maris din da ya gabata.
Shi dai Sadique ya tsaya wa jam’iyyar APC ce takara a zaɓen, amma ya yi rashin nasara a hannun Gwamna Bala Mohammed, kamar yadda Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana a wancan lokacin.
“We have confidence in the lots of evidence to present at the higher judicial stages. Insha Allah, we will reclaim our stolen mandate,” Abubakar added.