Ban gamsu da nasarar Tinubu ba, Kotun Koli zan tafi – Atiku
Ya ce sam bai gamsu da hukuncin kotun ba
Dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Atiku Abubakar, ya ce bai gamsu da hukuncin kotun sauraron kararrakin zabe na tabbatar da nasarar Shugaba Bola Tinubu ba.
Ya ce tuni ya bukaci lauyoyinsa da su shirya tafiya Kotun Koli domin daukaka kara.
- Takun-saƙar da ke tsakanina da Messi ta kare – Ronaldo
- Manyan mutanen da Tinubu ya sallama daga aiki
Atiku dai ya kalubalanci nasarar da Tinubu ya samu a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata, amma kotun ta yi watsi da ƙarar ta shi.
To sai dai da yake mayar da martani yayin taron manema labarai a hedkwatar PDP da ke Abuja, Atiku ya ce, “Na zo nan ne domin na fadi matsayina a kan hukuncin da kotun sauraron kararrakin zaben Shugaban Kasa na 2023 da aka yi jiya.
“Kamar yadda kuka sani, na kai kara kotu don na kalubalanci nasarar APC a zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairu. Duk wanda ya san ni, ya san ni mutum ne da ya yi amanna da bangaren shari’a.
“An san ni a matsayin wanda ba shi da tsoro, kuma mai jajircewa. Ni ba bako ba ne a bangaren kai kara, kuma ina kyautata musu zato.
“…tuni na umarci lauyoyina su yi nazarin hukuncin domin su garzaya Kotun Koli, domin daukaka kara,” in ji shi.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar ya kuma ce har yanzu yana nan a kan bakarsa cewa an tafka magudi a zaɓen da ya ba Tinubu nasara, amma duk da haka, ya ce rashin jin dadinsa ga hukuncin ba yana nuna ya yanke kauna ba ne da bangaren shari’a.