Ban gamsu da yadda Najeriya ta buga wasanta na farko da Iran ba -Musa Mai Nama

Wani masoyin kwallon kafa da ke goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Musa Mai Nama ya bayyana bacin ransa a kan yadda kungiyar ta kasa samun nasara a wasan da ta yi da Iran a ranar Litinin da ta wuce.Ya ce yadda ’yan kwallon suka kasa doke Iran ya nuna cewa da wuya […]

Ban gamsu da yadda Najeriya ta buga wasanta na farko da Iran ba -Musa Mai Nama
Ban gamsu da yadda Najeriya ta buga wasanta na farko da Iran ba -Musa Mai Nama

Wani masoyin kwallon kafa da ke goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles Musa Mai Nama ya bayyana bacin ransa a kan yadda kungiyar ta kasa samun nasara a wasan da ta yi da Iran a ranar Litinin da ta wuce.
Ya ce yadda ’yan kwallon suka kasa doke Iran ya nuna cewa da wuya Najeriya ta kai labari a gasar.  Ya ce idan aka yi la’akari da yadda Najeriya za ta hadu da manyan kasashe irin su Ajantina da kuma Bosniya Herzegobina a sauran wasannin a rukunin F, to da wuya kasar ta kai labari.
“Da ma Iran ita ce dama-dama da aka ganin Najeriya za ta iya lallasa wa a rukunin amma abin mamaki sai ga shi ta rike wa Najeriya wuya don haka akwai shakku a kan yiwuwar kungiyar ta kai labari a gasar”, inji shi.
Daga nan ya hori ’yan kwallon Super Eagles da su yi duk mai yiwuwa don ganin sun samun nasara a wasan da za su yi da Bosniya a gobe Asabar idan Allah Ya kai mu.
A tattaunawar da ya yi da Aminiya ta wayar tarho Musa ya ce a ranar da aka buga wasan Najeriya da Iran bai samu barcin kirki ba saboda bakin ciki.  Ya ce ya yi imani ba shi kadai abin ya shafa ba don akwai miliyoyin ’yan Najeriya da suka kwana da bakin ciki a kan wasan saboda bai yi musu dadi ba.
Sai dai ya yi fatan kungiyar za ta share wa daukacin ’yan Najeriya hawaye a sauran wasannin da suka rage a gasar don ganin sun ba marada kunya.
Idan za a tuna, kungiuyar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles ta yi canjaras ne da ta Iran a ranar Litinin da ta gabata a wasanta na farko inda aka tashi 0-0.
A gobe Asabar ne, idan Allah ya kaimu, Najeriya za ta sake karawa a wasanta na biyu da Bosniya Herzegobina.  Za a yi wasan ne da misalin karfe 11 na dare agogon Najeriya.