Ban gayyaci Tinubu don yin sulhu a rikicin Ribas ba —Wike

Wike da magajinsa Fubara sun sa zare inda alakarsu ta yi tsami a baya-bayan nan.

Ban gayyaci Tinubu don yin sulhu a rikicin Ribas ba —Wike

Ministan Birnin Tarayya, Nyesom Wike, ya ce bai gayyaci Shugaba Tinubu domin yin sulhu a rikicin siyasar Jihar Ribas ba.

Wike ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin bikin godiya ga tsohon kwamishinan ayyuka na Jihar Ribas, George Kelly Alabo, a Fatakwal.

A makon da ya gabata ne dai aka cimma matsaya tsakanin Wike da Gwamna Fubara da ke rikici da juna bayan ganawar da suka yi da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A lokacin ganawar, Wike ya yaba wa Shugaba Tinubu kan sa baki a rikicin, amma ya ce bai gayyace shi don yin hakan ba.

“Kai ne ka ce shugaban kasa ya sa baki, kuma ya sa baki. Yanzu ka juya ka ce ba shi da hurumi a tsarin mulki.

“Duk halin da ake ciki, ni shugaban ya gayyata ta ya yi taron. Na mika kaina ga tsarin zaman lafiya.

“Wasu daga cikinku ba su ma san cewa shugaban kasa ya gayyace mu a asirce ba. Dole ne mu fada wa mutanenmu gaskiya. Na yi nawa bangaren. Na yi iya yi na kuma ina farin ciki, a Abuja ma ina yin aiki mai kyau.”

Idan ba a manta ba Wike da Gwamna Fubara sun sa zare, inda alakarsu ta yi tsami.

Zaɓen Ondo: Wanda bai gamsu ba ya garzaya kotu — Tinubu

Lucky Aiyedatiwa ya lashe zaɓen Gwamnan Ondo

Ba na yi wa Tinubu hassada — Atiku

Kama matashiya kan sukar Gwamnan Sakkwato ya tayar da ƙura