Ban goyi bayan Buhari ya ja layi ga barayin kasar nan ba – dan Madamin Isah
Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Sakkwato Alhaji Usman Suleiman dan Madamin Isah a zantawarsa da wakilin Aminiya kan sabuwar gwamnatin Buhari ya bayyana fatarsa inda ya ce ba ya goyon bayan gwamnatin Buhari ta ja layi ga wadanda ake zargi da sace dukiyar kasar nan, kuma ya tabo tsare-tsaren gwamnatin jihar a karkashin Alhaji Aminu […]
Shugaban Jam’iyyar APC reshen Jihar Sakkwato Alhaji Usman Suleiman dan Madamin Isah a zantawarsa da wakilin Aminiya kan sabuwar gwamnatin Buhari ya bayyana fatarsa inda ya ce ba ya goyon bayan gwamnatin Buhari ta ja layi ga wadanda ake zargi da sace dukiyar kasar nan, kuma ya tabo tsare-tsaren gwamnatin jihar a karkashin Alhaji Aminu Waziri da sauransu:
Aminiya: An kammala zaben Shugaban kasa da na Gwamna yaya ka ji a lokacin da aka bayyana jam’iyyarka ce ta samu nasara a wadannan zabubbuka ganin akwai kalubale a gabanku?
dan Madami: To gaskiya na samu kwarin gwiwa saboda ni ban yi tsammanin Jam’iyyar PDP za ta samu nasara a wadannan zabubbuka ba. Maganar kalubale kuwa ba ka ganin kamar wanda ya kasance ba ya da gaba da baya ya fuskanci kalubale, balle yanzu shi yake da wuka da nama, komai zai tafi daidai za mu gyara makarantu da harkar noma da gina hanyoyi duk wadannan ba su da wani wahala ga wanda bai dauke kudin mutane ba, aiki kawai za mu yi wa mutane.
Aminiya: A kasar nan ba a taba kayar da jam’iyya mai mulki ba sai yanzu, me kake ganin ya ba ku wannan nasara?
dan Madami: Abin da ya ba mu wannan nasara shi ne mutanen Najeriya sun gaji da zaluncin da ake yi musu da kashe su da ake yi kullum, mutum 100 ko 200 ko 300 haka ake ji a coci-coci da masallatan Juma’a ana dasa bama-bamai amma gwamnati ta kasa daukar mataki, tattalin arzikin kasa ya lalace, sai da Dala ta kai Naira 240, da sauran abubuwan more rayuwa da talakan kasar nan ya rasa, kan wadannan ne da wasu da ban iya zayyanowa ba, suka sa talakawa suka yi tsaye suka samar da canji, ka ga kuma canji ya yi amfani domin kafin Buhari ya amshi ragamar jagoranci Dala ta koma Naira 180, Boko Haram sun daina tayar da bama-bamai.
Aminiya: Kana ganin karbar kaye da Shugaba Jonathan ya yi zai shafe bakin jinin da ya yi, ya dawo masa da martaba?
dan Madami: Eh! kwarai da gaske amincewa da faduwa a zabe da ya yi zai mayar da martabar kasar nan da shi kansa, wannan halin da ya aikata gaskiya ba a yi tsammanin wani dan Najeriya ya aikata hakan ba, salin alin tun kafin a kammala tattara kuri’un zabe, ba wai adawa za mu sanya ga wannan maganar ba, dole mu fadi gaskiya cewa Shugaba Goodluck ya yi rawar gani a wurin duk dan kasa nagari da ya san abin da yake yi. Karbar sakamakon zabe da zuciya daya ya samar wa kasa zaman lafiya kuma hakan ya nuna shi masoyin hadin kai ne da ci gabanta, magoya bayansa ne kawai ke sanya shi cikin abubuwan ta’asa, ina jinjina masa da yaba masa, ya nuna shi dattijo ne abubuwan da ke gudana a gwamnatinsa mukarrabansa ne ke dagula al’amura.
Aminiya: ’Yan Najeriya musamman talakawa na ganin tunda Buhari mai gaskiya ne da zarar ya karbi jagorancin kasar nan komai zai koma daidai mene n ra’ayinka kan wannan tunani?
dan Madami: To ka san tunani na ’yan kasar nan, amma ya yi daidai don ka duba kasuwar hada-hadar kasuwanci ta tashi, an samu riba ta fiye da Naira tiriliyan daya da samun nasarar Buhari kawai, yanzu kuma yana samun hadin kai ’yan Najeriya sosai don zamansa mai gaskiya wannan nasara ce. Ina tabbata maka ba sai an yi shekara hudu ba Muhammadu Buhari zai bunkasa arzikin Najeriya cikin shekara daya, kai ba ma wannan ba shekara daya ta Buhari kowane fanni a Najeriya zai zauna daidai. A ra’ayina kan samun nasarar gwamnatin Buhari a janye maganar jan layi in ba ga abubuwan gina kasa ba, malam yaya kake ganin mutum ya saci Naira tiriliyan daya ka ce a ja layi daga kansa, to wane layi za a ja tun da bai jawuwa, ba laifi dai a kira mutum a ce tunda ka saci kaza to kawo abin da ke gare ka a sanya a baitul mali ka tafi abin ka. Mene ne laifin haka, ko an kyale ka da su tunda an san ba ka iya cinye su, ka kai su kasashen waje dole Buhari ya sanya a dawo da su, ba mu ce a dauri kowa ba, in ka ga an daure ka to ba ka ba da hadin kai ba, jan layi bai yiwuwa a ce duk wadanda suka kwashi dukiyar jama’a sun sha banza ke nan. Shugaban kasa mai ci da mukarrabansa ba zai wahalar da su ba in suka bayar da hadin kai, ba na goyon bayan Buhari ya ja layi ga barayin kasar nan.
Aminiya: Kun samu nasara a Jihar Sakkwato wadanne tsare-tsare ne kuka shirya don ciyar da jihar gaba?
dan Madami: Ka san Mai girma Gwamnan Jihar Sakkwato Alhaji Aliyu Wamakko ya yi aiki sosai na ciyar da al’umma gaba, matsalar gwamnatinmu babu masu farfaganda a yi talla in aka yi aiki, shi mai girma Gwamna ayyukkansa tsakaninsa da Allah ne yake yi, mutane na yin alkalanci don haka ne ya sa duk wadanda ya tsayar takara suka samu nasara. Ina tabbatar maka wanda zai gaje shi, zai ci gaba da daga martabar wannan jihar iya gwargwado, domin Alhaji Aminu Tambuwal ya sha fadin cewa yadda Gwamna Alu ya yi wuya gare shi, amma zai kwatanta gwargwado, gefen noma ne da kasuwanci za a amfana da kirkiro masana’antu a kowane bangare da ka sani a jihar nan ba za a bar shi a baya ba.
Aminiya: Mene ne sakonka ga sabon Shugaban kasa?
dan Madami: Ina kira ga zababben Shugaban kasa ya gode wa Allah ga wannan ni’ima, ya yafe wa jama’ar da suka yi masa ba daidai, kuma duk wanda bai yi laifi ba kada laifin wani ya shafe shi. Magoya bayan jam’iyyarmu ta APC su yi hakuri da junansu don samun nasarar wannan tafiya.