Ban ji dadin sanya hotona a labarin rikicin Kannywood ba – Rahama Sadau
Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan yadda aka sanya hotonta a labarin da aka wallafa kan yadda batun biyan ‘yan fim wanda ya raba kan masana’antar. Jarumar dai ta nuna rashin jin dadin yadda a ka sa hotonta a labarin da aka wallafa a kan batun yadda biyan’ yan […]
Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan yadda aka sanya hotonta a labarin da aka wallafa kan yadda batun biyan ‘yan fim wanda ya raba kan masana’antar.
Jarumar dai ta nuna rashin jin dadin yadda a ka sa hotonta a labarin da aka wallafa a kan batun yadda biyan’ yan fim ya raba kan Kannywood, wanda ya samo asali tun bayan hirar da shashen ya yi da Ladin Chima, daya daga cikin jaruman na Kannywood .
- Na biya Ladin Cima N40,000 a fim din Gidan Badamasi —Nazir Salihi
- Kannywood ta dauki zafi kan maganar biyan hakkin ’yan wasa
Jarumar ta bayyana hakan a ne a kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana cewa ita ba tace komai ba a cikin wannan rikici amma kuma BBChausa sun sanya hotonta a cikin jerin wadanda rikicin ya shafa.
Jarumar dai ta sake wallafa labarin a Twitter tare da rubuta”To ni kuma mai ya kawo hotona ciki?, neman magana ko me?” a jikin labarin.
Wannan ya sa mutane dake bibiyar shafin tofa albarkacin bakinsu a kai, inda wasu ke ganin kafar BBC ta yi amfani da hoton nata ne domin jan hankalin masu karatu.
Sai dai kuma a cikin labarin, BBC ta bayyana yadda jarumar da ma wasu daban irin su Adam Zango suka nuna nuna alamar yin shiru, duk da sun nuna akwai magana.