Ban karbi ko kwabo daga hannun Shugaban INEC ba- Furodusan ‘Ibro Jega’
Sabanin maganganun da ke yawo a masana’antar fim din Hausa ta Kannywood cewa furodusan fim din ‘Ibro Jega’ ya samu gwaggwabar kyauta daga Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, furodusan fim din Muhammad Najeeb ya shaida wa Aminiya cewa bai karbi ko kwabo daga wurin shugaban Hukumar INEC din ba.Furodusa Najeeb ya bayyana […]
????????????????????????????????????

Sabanin maganganun da ke yawo a masana’antar fim din Hausa ta Kannywood cewa furodusan fim din ‘Ibro Jega’ ya samu gwaggwabar kyauta daga Shugaban Hukumar Zabe ta kasa Farfesa Attahiru Jega, furodusan fim din Muhammad Najeeb ya shaida wa Aminiya cewa bai karbi ko kwabo daga wurin shugaban Hukumar INEC din ba.
Furodusa Najeeb ya bayyana cewa ya gano batun jita-jitar ne a lokacin da ya yi ta samun sakonnin taya murna daga ’yan uwa da abokan arziki game da kyautar da ake cewa Farfesa Jega ya yi masa. “Na yi ta mamakin irin sakonnin da nake samu, sai da na tsananta bincike ne na gano cewa wasu mutane na ke ta yada jita-jita cewar Farfesa Jega ya kira ni ya yi min kyauta game da fim din ‘Ibro Jega’ da na shirya. Bari na yi amfani da wannan damar na bayyana cewa duk da cewa fim din ya samu karbuwa a wurin ’yan kallo zan iya bugun kirji na ce ban samu komai a fim din ba, don har yanzu kokari nake na ga uwar kudina ta dawo, ba a maganar riba.” Inji shi.
Furodusan ya kara da cewa duk da cewar bai karbi wani kudi ba, yana da labari daga majiya mai tushe cewa Shugaban INEC din ya bayar da wasu kudi masu kauri don a ba shi: “wata majiya mai tushe ta shaida min cewa wasu mutane sun je sun karbi kudi da sunana daga wurin Farfesa Jega wanda kuma har zuwa yanzu da muke magana da ku ban sami ko kwabo ba” Inji Najeeb.
Sai dai Furodusan ya bayyana cewa hakan ba zai hana shi ci gaba da aiwatar da jihadin da ya fara na kokarin fadakarwa da kuma gyara halayen ‘yan Najeriya ta hanyar fim ba.
A cewarsa ya yi nisa wajen shirya fina-finai wadanda suke nuni da girmama shugabanni wadanda suka yi wa kasa hidima a maimakom yin alla-wadai da su a kowane lokaci.