‘Yadda muka fara wasan kwaikwayon Karkuzu na Bodara’
Yadda aka fara wasan kwaikwayon Karkuzu na Bodara da abin da ya sa aka dakatar da shi.
Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Karkuzu na Bodara, tsohon dan wasan kwaikwayo ne wanda har yanzu ake damawa da shi a harkar fina-finan Hausa.
Wasan kwaikwayonsa na Karkuzu na Bodara daya ne daga cikin wadanda suka fi tashe a cikin jerin wasannin da gidan talabijin na kasa (NTA) ya gabatar a shekarun baya.
- Fina-finan Hausa na daf da fitowa a Netflix –Alhaji Sheshe
- Budurwa ta mutu suna tsaka da fasikanci a cikin mota
A wannan tattaunawa da ya yi da wakilinmu, ya bayyana yadda aka fara fitaccen wasan kwakwayon na Karkuzu na Bodara da wasu muhimman abubuwa a game da wasan da ma yadda ya tsunduma masana’anar fina-finan Kanywood da sauransu.
Ku biyo mu:
Ka gabatar mana da kanka.
Sunana Abdullahi Shu’aibu, wanda aka fi sani da Abdullahi Karkuzu na Bodara. Ina zaune a nan garin Jos kkuma yanzu ina da shekara 68 da haihuwa.
A wanne lokaci ne ka fara wasan kwaikwayo?
Na fara wasan kwaikwayo ne tun zamanin mulkin tsohon Shugaban Kasa, marigayi Alhaji Shehu Aliyu Shagari.
Ka fara shahara ne a wasan kwaikwayo na ‘Karkuzu na Bodara’, yaya aka fara wannan shiri?
To wannan shiri na ‘Karkuzu na Bodara’, mun fara yin shi ne a bakin titi, a wannan gari na Jos kamar misalin karfe 8 na dare, sai mu zo mu shimfida tabarmi, sai a raba wa kowa abin da zai yi; a ce kai wane kai ne barawo, wane kai ne dillali wane kai ne dan caca, wane kai ne alkali, da haka muka fara wannan wasan kwaikwayo. Daga baya, sai kuma muka koma yi a talabijin.
Mace ce ma’anar Karkuzu?
Ma’anar sunan karkuzu shi ne mutum mai ban dariya, kuma wannan suna ya samo asali ne daga sunan littafin da muka karanta wajen shirya wannan wasan Kwaikwayo, da ake kira Ar’us. Sai muka canza shi ya koma Karkuzu.
A littafin kuma Bodara ita ce matar Ar’us, don haka sai muka mayar da sunan, ya koma Karkuzu na Bodara.
Baya ga wannan wasan kwakwayo na Karkuzu a wane wasan kwaikwayo ne ka fito?
Gaskiya na fito a wasannin kwaikwayo da yawa, bayan wannan wasan kwaikwayo na ‘Karkuzu na Bodara’.
An zo an dauke ni daga wurare daban-daban, kamar wasan kwaikwayo na Samanja da wasu wasannin kwaikwayo na Kasimu Yaro da wasan kwaikwayo na Dan Wanzam na Sakkwato da wasan kwaikwayo na Karo da Goma daga Kano da wasan kwaikwayo na Kowanne Gauta Ja ne daga Bauchi da dai sauransu.
Zuwa yanzu ka fito a wasannin kwaikwayo kamar nawa?
Gaskiya ba zan iya kirga yawan wasannin kwaikwayon da na fito ba. Domin idan na ce na fito a wasannin kwaikwayo 100 ko 10 ko 30 na yiwa kaina karya.
Gaskiya na fito a wasannin kwaikwayo da yawa amma ban san adadin yawansu ba.
Cikin wadannan wasannin kwaikwayo a wanne ne ka fi burgewa?
Akwai wasannin kwaikwayo da nafi burgewa. Wasan kwaikwayo da nafi burgewa shi ne akwai wani lokaci a cikin shirin da muke yi da matata, Bodara.
Na ce Bodara? ta ce na’am, na ce ni fa talauci ya ishe ni, don haka zan canza sana’a.
Ta ce wace sana’a zaka yi? Na ce zan shiga aikin soja. Ta ce kai yanzu da tsufar nan naka, waye zai dauke ka aikin soja? Na ce ko ba a dauke ni aikin soja ba, ni zan dauki kaina da kaina.
To dama abin da na kudurta a raina, sojan gona zan shiga, wato sojan rashin gaskiya masu bata wa sojoji suna.
Wannan wasa ya yi matukar burge ni.
Yaya za ka kwatanta wasannin kwaikwayo na da na yanzu?
Gaskiya wasan kwaikwayo da da na yanzu ba iri daya ba ne. Domin wasannin kwaikwayon da muke yi a da ba mu shiga don neman kudi ba.
Domin duk kudin da ake biya na a wannan wasan kwaikwayo na Karkuzu, a matsayina na jagora Naira 6 ake biya na. A yanzu kuwa babu yadda za a yi a ce za a dauke ni, na je na yini ina aiki a kawo Naira dubu 10 a ba ni.
Ina da ina ne ka je a dalilin wasannin kwaikwayo?
Sanadin wasan kwaikwayo babu jihar da ban je ba a Najeriya. Na zagaya jihohin Najeriya guda 36 har da Abuja babban Birnin Tarayyyar Najeriya.
Wadanne ’yan wasa ne ka fi jin dadin wasa da su?
A yanzu dai da muke yin fim ake zuwa a dauke ni, a je a ba ni abin da zan yi, kowane dan wasa aka hada ni da shi, in Allah Ya yar da zan yi aiki da shi.
Kuma kowanne dan wasa aka hada ni da shi, ina jin dadin wasa da shi.
Wane Darakta ko Mai shirya fim ne kafi son fitowa a fim dinsa?
Wallahi suna da yawa. Domin duk Daraktocin fina-finan nan, kowanne na yi aiki da shi kuma babu wanda ya wulakanta ni, ni ma babu wanda nake wulakantawa.
Yaya dangantakarka da tsofaffin ’yan wasa irin su Magaji Mijinyawa da su ma suka fito a wasan kwaikwayo na gidan talabijin n akasa (NTA)?
Magaji Mijinyawa mun yi aiki da shi a NTA, domin a NTA ne muka fara wasan Karkuzu. Don haka a lokacin da muke wannan wasa, Magaji Mijinyawa sananne a wajena, ni ma sananne a wajensa.
Wane dalili ne ya sa aka daina wasan kwaikwayo na Karkuzu?
A lokacin tsohon gwamnan farar hula na farko a Jihar Filato, marigayi Solomon Lar da ya ga abubuwan da muke yi, a wannan wasan kwaikwayo na Karkuzu na Bodara, na wayar da kan al’ummar Jihar Filato, kuma jama’a suna jin dadin wannan wasan kwaikwayo, sai ya ba ni kudi N8,600 muka je muka sayi mota Fijo sabuwa fil.
Sai Janar Manajan NTA na Jos na lokacin, ya ga kamar Solomon Lar yana son na rika yi masa aiki a wannan wasan kwaikwayo ne, shi ya sa ya ba mu kudi muka sa yi wannan mota.
Shi kuma Lar ya ba mu wannan mota ne saboda jin dadin wasan da al’ummar jiharsa suke yi kuma shi da kansa yana kallon wannan wasa, yana jin dadi, don haka ya ba mu wannan mota, domin ya karfafa mana gwiwa.
Kasan a lokacin, tun da su suna karkashin Gwamnatin Tarayya ne, ita kuma Gwamnatin Tarayya jam’iyyar NPN ce take mulki. Shi kuma marigayi Gwamna Lar, yana jam’iyyar NPP ne.
Ni kuma a lokacin sai na ce da Janar Manajan, ba zan iya daukar motar nan na mayar wa da Gwamna Lar ba.
Sai ya ce ko dai mu mayar da motar, ko kuma su rufe wannnan wasan kwaikwayo da muke yi.
Ni kuma da sauran abokan aikina muka tashi a dakin taron da muka yi, muka ce ba za mu mayar da motar ba, shi kuma ya ce za su rufe wannan wasan kwaikwayo na Karkuzu na Bodara.
Ni kuma na ce su rufe, kaji dalilin da ya sa aka daina wasan Karkuzu na Bodara a NTA.
Daga nan sai marigayi Solomon Lar, ya gina gidan Tilbijin na PRTB, a lokacin yasa aka bamu fili muka cigaba da wannan wasa. Muna nan muna aiki a PRTB, sai da Allah ya kawo wani lokaci da muka shiga, wani hali a wannan jiha, wanda ya kai ga aka daina yin wannan shiri, a wannan tasha ta PRTB.
Shin a wannan lokacin ne ka fara fitowa a fina-finan Kanywood?
To, fina-finan Kanywood, bayan an rufe wannan wasa na Karkuzu a PRTB, sai na koma fitowa a fina-finan Kanywood.
A wanne fim ne ka fara fitowa a Kanywood?
Akwai wani fim wanda ake kiran sa Sarauta, wanda Ali Nuhu ya zama dana juma ina son sa na rika wahala da shi. Wannan shi ne fim da na fara fitowa a Kanywood.
Wane fim ne ka yi burin ina ma ace ka fito a cikinsa?
To ni babu wani fim da Kanywood suka yi ko kuma wani Darakta ya yi da zan ce nayi sha’awar da ma ace na fito a cikinsa.
Ni dai kowane fim aka saka ni zan shiga na taka rawata, idan ba a kira ni ba kowane irin fim ne bana zuwa.
A lokuta da dama ana samun takaddama a masana’antarku ta Kanywood, inda ake zargin wasu da aikata ba daidai ba, wani zai ce a matsayinku na manya, kuna ina ake aikata irin wadannan abubuwa?
Wato maganar rigingimu na masana’antar Kanywood ba na shiga ciki, saboda rigingimu ne na neman girma. Ni dai idan za ayi fim, aka zo aka dauke ni, aka ba ni abin da zan yi, sai na yi abin da aka ce na yi, a biya ni.
Wane irin alfanu ne kake ganin ka samu a wannan harka ta wasan kwaikwayo?
Wallahi na sami alfanu da dama, a wannan harka ta wasan kwaikwayo, domin duk ofishin wani kwamishina ko minista ko wani darakta ko wani ofishin gwamnati, zan ga duk wanda na je wajensa, zan samu ganin sa, ba tare da bata lokaci ba.
Yanzu matanka nawa da ‘yayanka?
Matata daya ce da ’ya’ya bakwai amma guda biyu sun rasu.
A cikin ’ya’yanka akwai masu yin fim?
Babu mai yin fim a cikin ’ya’yana.
Kana cikin ’yan wasan kwaikwayon da suka fi yawan shekaru yanzu, yaushe za ka yi ritaya?
Ritaya daga wasan kwakwayo ritaya ce tawa ta kaina, ba ta gwamnati ba, ballantana a ce an yi mani ritayar.
Ni ne zan yi wa kaina ritaya, idan zan yi. Amma a yanzu ban taba sa ranar da zan yi ritaya daga wasan kwaikwayo ba, domin ba abu ne nake yi mummuna ba. Abu ne wanda bai saba wa ka’ida ba.
Idan ma na mutu a cikinsa na gode Allah. Don haka ban sa ranar da zan yi ritaya daga wasan kwaikwayo ba.
Kwanan baya an yi ta yada jita-jitar cewa an kore ka daga gidan da kake haya, mece ce gaskiyar wannan magana?
Tabbas an yi haka. Kasan idan mutum yana zaune a gidan da ba nasa ba, idan maigidan ya bukaci ka ba shi gidansa, ya ba ka notis dole ka fita ka bar masa gidansa.
Ni dai har yanzu da muke magana da kai bani da gidan kaina, kai ko daki daya ba ni da shi a nan Jos. Amma idan Allah Ya kawo zan yi.
Domin da ma koken da nake ta yi ke nan, kan Allah Ya kawo wanda zai taimaka mani ko da daki hudu ne ko daki biyar a ce wannan nawa ne.
Da ma abin da nake bukata ke nan, wani ya yaye mani wannan bakin ciki, shi ke nan ko da mutuwa na yi a ce a gidana ’ya’yana suke karbar ta’aziyar rasuwata. Wannan shi ne babban burina.