Ban samo matar aure ba a Ghana – Osita Iheme
dan wasan barkwanci da yake fitowa a fina-finan Kudancin Najeriya, Osita Iheme, wanda kuma ake ganin ya dade bai yi aure ba ya ce shi bai samo wata matar aure ba a ziyarar da ya kai kasar Ghana. Osita ya fito fili ya bayyana haka ne, a sakamakon yadda aka shiga yada jita-jitar cewa ya […]
dan wasan barkwanci da yake fitowa a fina-finan Kudancin Najeriya, Osita Iheme, wanda kuma ake ganin ya dade bai yi aure ba ya ce shi bai samo wata matar aure ba a ziyarar da ya kai kasar Ghana.
Osita ya fito fili ya bayyana haka ne, a sakamakon yadda aka shiga yada jita-jitar cewa ya samu matar da zai aura a Ghana. Baya ga jita-jitar, an rika nuna hotunan dan wasan ne tare da wata ’yar fim da ke Ghana mai suna Nana.
dan wasan, wanda bai dade da wallafa littafinsa na farko ba mai taken Inspired 101, ya bayyana wa mujallar Encomium cewa, ba kamar yadda ake yamadidi da shi cewar zai yi aure ba, ya ce har yanzu shi gwauro ne. “Ban fara soyayya da kowa ba.” Inji shi, inda ya ce matar da ake cewa zai aura ba gaskiya ba ne, sun yi aikin daukar fim ne kawai tare amma ba soyayya ba.
Ya ce shi bai da wani kuduri ko sha’awar zuwa Ghana domin ya yi aure. “Ba na tunanin tafiya kasar Ghana da nufin yin aure a can. “Babu shakka mutum zai iya zuwa ko’ina ya hadu da matar da zai aura, amma dai a yanzu ni ban samu wata mata da zan aura a Ghana ba. Abin da ya faru shi ne, matar da aka gan mu tare a Ghana, mun yi aikin daukar fim tare da ita ne, amma babu soyayya a tsakaninmu.” Inji shi.