Ban san cewa Sufeto Janar na ‘yan sanda bai tare a Binuwe ba- Shugaba Buhari
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ban san cewa sufeto janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris bai tare a Jihar Binuwe ba duk da cewa ya ba shi umarnin yin hakan. Shugaban ya yi wannan bayanin cikin mamaki a Jihar ta Binuwe a lokacin da ya kai ziyara jihar tare da yi wa mutanen […]

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ban san cewa sufeto janar na ‘yan sanda Ibrahim Idris bai tare a Jihar Binuwe ba duk da cewa ya ba shi umarnin yin hakan.
Shugaban ya yi wannan bayanin cikin mamaki a Jihar ta Binuwe a lokacin da ya kai ziyara jihar tare da yi wa mutanen jihar jaje kan rikicin makiyaya da manoma.
“ban san cewa sufeto janar na ‘yan sanda bai tare a Jihar Binuwe ba kamar yadda na ba shi umarni.
Daga bisani Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa ba za su nade hannu suna kallo abubuwa na faruwa ba ba tare da sun dauki mataki, inda ya tabbatar da cewa suna yin aiki tukuru domin kawo karshen zubar da jinni da ke gudana a jihar.