Ban san Gowon ne ya hana Abacha kashe ni ba — Obasanjo

Obasanjo ya ce duk waɗannan shekaru da aka shafe bai san cewar Gowon ne, ya ceci rayuwarsa ba.

Ban san Gowon ne ya hana Abacha kashe ni ba — Obasanjo

Tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya yi wa Janar Yakubu Gowon (mai ritaya), godiya kan yadda ya roƙi Marigayi Janar Sani Abacha don ya bar shi da rai a lokacin mulkinsa.

Obasanjo, wanda aka ɗaure a gidan yari kan zargin yunƙurin yi wa Abacha juyin mulki, ya ce ba shi da masaniyar kan rawar da Gowon ya yi aka bar shi da ransa.

“Ina so na yi wa Shugabana godiya, Janar Yakubu Gowon. Jiya ka yi wani bayani, kuma dole ne na gode maka.

“Bayan na fito daga gidan yari, na samu damar yi wa abokaina da waɗanda suka yi ƙoƙari wajen sakina, godiya.

“Kuma na zagaya duniya ina yi wa waɗanda suka sa baki da waɗanda suka taya ni addu’a, godiya.

’Amma ban san cewa ka rubuta wasiƙa ta musamman don a sake ni ba, sai da ka faɗa jiya; na gode maka kan hakan,” in ji Obasanjo.

Gowon, ya bayyana yadda ya taka rawar gani wajen sakin tsohon shugaban ƙasar.

Ya ce ya rubuta wa Abacha wasiƙa, inda ya roƙe shi don a tausaya a saki Obasanjo.

Gowon, ya bayyana cewa ya bai wa matarsa wasiƙar, wadda ta kai ta kai wa Abacha da kanta cikin dare a Abuja.

Ya bayyana farin cikinsa cewar bayan Obasanjo, ya kwashe shekaru uku a gidan yari, an sake shi bayan mutuwar Abacha a watan Yunin 1998, sannan daga baya ya zama Shugaban Ƙasa a 1999.

Gowon ya bayyana haka ne, yayin wani taron ƙarshen shekara da aka fara ranar Juma’a zuwa Lahadi a Jihar Filato.

Taron ya samu halartar Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, tsoffin gwamnonin jihar kamar Jonah Jang, Joshua Dariye, Boni Haruna, da wasu manyan baƙi.

Obasanjo, ya kuma yaba wa Gwamna Mutfwang kan ayyukan ci gaba da ƙoƙarin samar da zaman lafiya a jihar.

Obasanjo ya kuma ruwaito yadda shi da marigayi Murtala Mohammed, suka yi wa Gowon juyin mulki a ranar 29 ga watan Yulin 1975.

Zazzaɓin Lassa: Mutum 190 sun mutu, 1,154 sun kamu a 2024 – NCDC

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu 7 a Adamawa

Arewacin Najeriya bai dogaro da wani yanki ba – Ndume

Jagoran Syria ya sha alwashin kwance ɗamarar ƙungiyoyin da ke rike da makamai