Ban san yadda aka yi kusa ta shige kaina ba – Mai shekara 60

Wani mutumin kasar Biyatnam (bietnam) ya kwashe kwana biyu da kusa a cikin kansa, inda daga baya ya je asibiti kuma ya ce bai san yadda aka yi kusar ta shiga kansa ba. Mutumin mai suna bu ban Tho, mai shekara 60, ya je asibitin sojoji na 354  ne da ke babban birnin Hanoi na […]

Ban san yadda aka yi kusa ta shige kaina ba – Mai shekara 60

Wani mutumin kasar Biyatnam (bietnam) ya kwashe kwana biyu da kusa a cikin kansa, inda daga baya ya je asibiti kuma ya ce bai san yadda aka yi kusar ta shiga kansa ba.

Mutumin mai suna bu ban Tho, mai shekara 60, ya je asibitin sojoji na 354  ne da ke babban birnin Hanoi na kasar bietnam.

Likitan da ya duba shi, Dokta Le ya ce yana cike mamakin yadda mutumin ya kwashe kwana 2 kafin ya je asibiti, sannan yana cikin hayyacinsa, kuma babu ko digon jini. 

Hoton kan mutumin ya nuna yadda kusar ta shige cikin kansa, kamar an buga masa kusar. kusar inci 3 ce, kuma hoton da aka dauka a asibiti ya nuna cewa ta shiga sosai.

Ko da aka tambaye shi yaya aka yi kusa ta shiga kansa, bu ban ya ce shi ma bai sani ba, sannan an gwada kwakwalwarsa lafiya ba ya da wata alamar hauka, kuma ba ya da niyyar kashe kansa.

A shekarar 2006 ma an taba samun irin wannan matsalar inda wani kafinta mai suna Nitin bishwakarma ya buga wa kansa kusa bisa kuskure a Mumbai na kasar Indiya.

Maimakon ya je asibiti a duba shi, sai kawai ya sha maganin zazzabi ya ci gaba da aikinsa. Sai daga baya da zazzabin ya yi zafi ne, ya je asibiti inda likitocin suka yi mamakin yadda ya rayu na kwanaki da kusa a cikin kansa. Sun dauki kusan awa uku suna yi masa aiki kafin su cire kusar.

Likitan da ya jagoranci cire kusar a wancan lokacin, Dokta Pramod Kubade, shi ma ya yi matukar mamakin yadda hakan ya faru, kuma mutumin ya ci gaba da rayuwa bayan an cire kusar daga cikin kansa.