Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio

Akpabio dai ya dage don kare kansa daga zarge-zargen da Sanata Natasha ke masa.

Ban taɓa cin zarafin Natasha ba, ina girmama mata — Akpabio

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya nesanta kansa daga zargin cin zarafin Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, inda ya ce mahaifiyarsa ta ba shi tarbiyya mai kyau, kuma yana mutunta mata.

Akpabio ya bayyana hakan ne bayan da Sanata Natasha ta zarge shi da cin zarafinta ta hanyar neman kwanciya da ita, wanda ya haifar da rikici a zauren majalisa.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce: “Ina son duniya ta sani cewa ban taba cin zarafin Sanata Natasha ko wata mace ba. Mahaifiyata ta yi min tarbiyya mai kyau, ina girmama mata.”

Wannan bayani na Akpabio ya zo ne a yayin da ake ta cece-kuce kan rikicinsa da Sanata Natasha, wanda ya samo asali daga zargin da ta yi masa kan wasu abubuwa da suka faru a baya.

Rikicin ya ɗauki sabon salo a zauren majalisar bayan da aka buƙaci ta sauya wajen zama, wanda ta ƙi amincewa da shi.

A zaman majalisar na baya, Sanata Natasha ta tsaya kai da fata tana kare kanta, inda ta nuna rashin amincewarta da matsin lamba da ta ke fuskanta.

Wannan ya jawo ruɗani a majalisar har aka buƙaci jami’an tsaro su fitar da ita daga zauren.

Sai dai, a cikin bayaninsa, Akpabio ya ce ba ya gaba da Sanata Natasha, kuma yana girmama mata a kowane hali.

Ya ce: “Tun daga yarinta, an koya min daraja mata, kuma a matsayina na jagora, ba zan taɓa nuna wariya ko cin zarafi ga kowace mace ba.”

A yanzu, jama’a na ci gaba da bibiyar wannan rikici don ganin yadda za a warware shi, yayin da ‘yan majalisa ke ƙoƙarin shawo kan lamarin domin kada rikicin ya ƙara ta’azzara a cikin majalisar dattawa.