Ban taba da-na-sanin shiga harkar fim ba-Rukayya Tijjani

Rukayya Tijjani Ayagi ba ta dade a harkar fim ba, amma ta fito a manyan fina-finai, inda a yanzu tana daya daga cikin jarumai mata da ake damawa da su a harkar. Ta yi bayani yadda ta fara harkar fim, matsalolin da ta fuskanta da nasarorin da ta cimma da kuma burinta nan gaba a […]

Ban taba da-na-sanin shiga harkar fim ba-Rukayya Tijjani
Ban taba da-na-sanin shiga harkar fim ba-Rukayya Tijjani

Rukayya Tijjani Ayagi ba ta dade a harkar fim ba, amma ta fito a manyan fina-finai, inda a yanzu tana daya daga cikin jarumai mata da ake damawa da su a harkar. Ta yi bayani yadda ta fara harkar fim, matsalolin da ta fuskanta da nasarorin da ta cimma da kuma burinta nan gaba a harkar. Ga yadda hirar ta kasance:

Za mu fara da tarihinki a takaice?
Sunana Rukayya Tijjani Ayagi, an haife ni a Kano. Na yi makarantar firamare da sakandare a Kano. Daga nan ban ci gaba da karatu ba, amma dai na ci gaba da zuwa makarantar Islamiyya.
Me ya ja hankalinki kika fara harkar fim?
Tun ina karama nake kallon fina-finan Hausa, hakan ya sanya na fara sha’awar in kasance daya daga cikin masu shirya fina-finan Hausa, wato a matsayin jaruma ko dai daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkar. Nakan fada wa mahaifiyata burina in zama jaruma, a lokacin ba ta cewa komai face ta yi dariya, domin ta dauka yarinta ce, amma har cikin zuciyata burina ke nan, abin da ban tambayi kaina ba shi ne, wace hanya ko mataki zan bi don shiga Kannywood. Na dai ci gaba da fada wa mahaifiyata, amma ba ta taba dakatar da ni ba, abin da take cewa shi ne, “yata a kowace sana’a a rayuwa akwai mutanen kirki da kuma bata-gari, amma ina da yakinin ba za ki taba zama daga cikin bata-gari ba, idan har harkar fim kike so ki yi, to ina miki addu’ar samun nasara.” A lokacin ma ban yanke shawarar fara harkar fim ba har na yi aure, kodayake aurena ya mutu tun ba a je ko’ina ba. Na yi dukkan hakurin da zan yi don ganin aurena bai mutu ba, amma abin ya ci tura, jim kadan bayan na haifi ’yata ne auren ya mutu. Daga nan ne na roki iyayena su amince in shiga harkar fim. Bayan sun amince ne sai shiga harkar gadan-gadan.
Wadanne matsaloli kika fuskanta?
Zan iya cewa ban fuskanci matsaloli masu yawa ba, kasancewar tun a farko iyayena sun amince mini. Ba wani abin boye-boye ba ne cewa yawanci mutane suna ganin ’yan fim a matsayin bata-gari, inda suke sukar su ba tare da kwararan hujjoji ba, hakan ya sanya ’yan uwa da abokan arziki suka ki amincewa in shiga harkar fim, amma sakamakon yadda na kare mutuncina sai suka fahimci ina cikin sana’a mai kyawu ce, sannan suka rika yi mini addu’ar samun nasara a harkar.
A kullum ina cikin farin ciki sakamakon sa’ar iyaye da na yi masu fahimta, sun ce mutum zai kasance na banza ne idan ya zabi kasancewa hakan. Abin da ya ba mutane mamaki shi ne, ban sha wahala wajen zama jaruma ba, kamar yadda sauran jarumai masu tasowa suka fuskanci kalubale sosai, sannan manyan harkar sun karbe ni hannu bibbiyu.
Yaya kika ji a ranar farko da aka dora miki kyamara?
Na ji wani iri, sai na ji kamar ina cikin mawuyacin hali, na fada wa kaina wannan ne lokacin da zai tabbatar da ko dai in burge furodusa da darakta ko kuma akasin haka. Na yi sa’a daraktan ya rika cewa in kwantar da hankalina. Daga baya jama’a suka rika fada mini na yi kokari, domin ba su taba tsammanin sabuwar jaruma za ta kokarin da na yi ba, inda na ci gaba wanda a yanzu ban san yawan fina-finan da na yi ba.
Wadanne fina-finai kika yi?
Kamar yadda na fada tun a farko, ina kallon kaina a matsayin jarumar da ta taki sa’a, domin cikin dan kankanen lokacin da na yi a harkar fim na yi fina-finai masu yawa da ya fi na sauran jaruman da na tarar a harkar. A yanzu da nake magana ba zan iya kirga yawan fina-finan da na yi ba. Fina-finan da na yi sun hada da ‘Hanyar Abuja’ da ‘Ranar Suna’ da ‘Gidan Haya’ da ‘Auren Soja’ da sauransu. Ni ce babbar jaruma a fim din ’Yan Bodin.
Me yake sa ki farin ciki idan aka ambaci harkar fim?
An ba ni kyaututtuka masu yawa, wadansu ma daga wurin mutanen da ban san su ba, ban taba ganin su ba. Sukan fada mini cewa sun ga fina-finaina ne, rawar da na taka ta burge su. Duk ranar da aka ba ni kyauta, ko aka yaba mini sakamakon rol din da na taka a wani fim sai in ji farin ciki ya lullube ni.
Ko kin taba da-na-sanin shigar harkar fim?
Ban taba da-na-sanin shiga harkar fim ba, ina so sana’ar sosai.
Wane buri kike da shi a harkar fim?
Burina in kasance daya daga cikin manyan jarumai, wanda tarihi ba zai taba mantawa da su ba. Ina so in yi wani abu da zai gyara rayuwar jama’a ta hanyar fina-finan da zan rika yi, wanda hakan zai sa a rika tunawa da ni. Ina so ’yan baya su rika koyi da ni, sannan su rika alfahari da ni.
Yaya batun aure kuma?
A yanzu dai babu batun aure saboda ba ni da manemi. Ina tare da wani amma a yanzu mun samu sabani.