Ban taba sha’awar rubuta littafin da ba na addini ba – Malam Aliyu Mainagge
Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge matashin malamin addinin Musulunci ne, wanda ya yi fice wajen rubuta littattafan addini. Aminiya ta tattauna da shi dangane da abin da ya shafi harkokinsa na rubuce-rubuce da kuma rayuwarsa. Ga yadda tattaunawar ta gudana: Mene ne tarihinka a takaice? Sunana Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, a gida ana kira […]
Malam Aliyu Ibrahim Sani Mainagge matashin malamin addinin Musulunci ne, wanda ya yi fice wajen rubuta littattafan addini. Aminiya ta tattauna da shi dangane da abin da ya shafi harkokinsa na rubuce-rubuce da kuma rayuwarsa. Ga yadda tattaunawar ta gudana:
Mene ne tarihinka a takaice?
Sunana Aliyu Ibrahim Sani Mainagge, a gida ana kira na Ali Baba ko Baba Ali saboda an sanya mini sunan kakana ne. An haife ni a Unguwar Sani Mainagge da ke Karamar Hukumar Gwale a Jihar Kano kimanin shekara 40 da suka gabata. Na halarci makarantar Alkur’ani ta Malam Umaru Bakatsine, wanda shi ne malaminmu na farko (Allah Ya kara masa lafiya) da Malam Kamilu da ke nan unguwarmu ta Sani Mainagge, inda na kammala saukar karatun Alkur’ani Mai girma. Sannan na yi karatun addini a wurin malamai masu yawa da suka hadar da; Malam Lawan Tela da Malam Sani Aliyu Sani Mainagge da Malam Yahaya Hasan Gwale da Malam Muhammad Aminu Sani Mainagge. Haka na yi karatu a wuraren wadansu malamai da suka hada da; Malam Isma’ila Sabon Titi da Gwani Malam Rufa’i Uba Hamza Gabari, da Dokta Ibrahim Mu’azzam Mai Bushra, Shugaban Sashen Addini da Shari’a na Jami’ar Bayero ta Kano da kuma Malam Baffa Aminu, tsohon Daraktan Sashen Addinin Musulunci na Ma’aikatar Ilmi ta Jihar Kano. Dukan wadannan malamaina ne kuma ina alfahari da su kwarai da gaske.
A bangaren boki, na halarci Makarantar Firamare ta Maitasa da Karamar Sakandaren Sabuwar Kofa da Kwalejin Horar da Malamai ta Gwale da Babbar Sakandaren Gwauron Dutse da Jami’ar Bayero, Kano, inda na yi digiri na farko a Ilimin Addinin Musulunci da Tarihi, tun daga shekarar 1996; kimanin shekara ashirin ke nan zuwa yanzu ina aiki da Hukumar Kananan Hukumomi ta Jihar Kano, inda nake aiki a halin yanzu a sashen walwala da jin dadin jama’a.
Haka kuma ni malamin Makarantar Islamiyya ne na shekaru masu yawa, inda na yi koyarwa a Makarantun Tarbiyyatul Umma, Gyadi-Gyadi da Anas Ibn Malik Sani Mainagge da Khadi Ahmad Islamiyya Rimin Gata, duk a garin Kano;, sannan ni na kafa Makarantar Darul Imara da ke Unguwar Sani Mainagge.
Haka kuma a shekarar 2014, na kafa kamfanin wallafa na AMBABA PRESS, kamfanin da ke wallafa tare da fassara da gyara littattafai (Editing) a harshen Larabci da Ingilish0i da Hausa.
A bangaren iyali, ina da mata da ’ya’ya shida rayayyu.
Tun yaushe ka fara harkar rubutu? Kuma me ya ja hankalinka ka fara rubuce-rubucen littattafan Musulunci?
Kamar yadda na taba fada wa gidan rediyon RAHMA da ke Kano, tun ina makaranta Allah Ya sanya mini sha’awar karatu, wanda kuma shi ya haifar da kasancewata marubuci. Babban abin da ya ja hankalina zuwa ga rubutu, musamman littattafan addini shi ne tasirantuwa da ayyukan ci gaban addini da kuma taimakon al’ummarmu. Ban taba yin sha’awar yin rubutu da ba na addini ba.
Wane littafi ne ka fara rubutawa kuma ya shiga kasuwa?
Na fara rubuta littafina na farko kimanin shekara ashirin da suka gabata. Littafin da na fara rubutawa shi ne ‘Siffofin Mutanen Kirki’ amma Allah bai sanya ya ga hasken rana ba, har takardun suka bace.
Zuwa yanzu littattafai nawa ka rubuta?
Bayan wancan littafi na ‘Siffofin Mutanen Kirki’ sai na rubuta littafin ‘Tafarki Madaidaici A Cikin Sanin Ilimin Alkur’ani.’ Littaffi ne da ke magana a kan Alkur’ani da iliminsa da siffofinsa da falalar karanta shi da kira’o’i da makamantansu. Shi wannan littafin ya fita kuma al’umma da yawa suna amfana da shi.
Haka kuma mun yi hadin gwiwa ni da Malam Usman Musa Gabari (Khalifa), muka rubuta littafin tarihin Manzon Allah (SAW) mai suna ‘Muhammad (SAW) Rahama Ga Talikai’ littafin da Farfesa Auwal Abubakar na Jami’ar Bayero ta Kano a gabatarwar da ya yi masa, yake cewa: “Shi ne irinsa na farko a harshen Hausa.” Daga nan sai littafin ‘Halifofi Shiryayyu.’ Shi kuma yana ba da tarihin Halifanci na shekara 30, kuma jaridar Albishir ta kamfanin Triumph ta rika buga littafin a wasu shekaru da suka gabata. Sai littattafan ‘Mafifitan Mutane Sahabbai (100) na maza da mata, littattafan da Allah Ya sanya musu albarka kwarai da gaske, al’umma masu yawa suka amfana da su. Sai ‘Tarihin Zababbun Mutane Annabawa (25), wannan har yanzu bai fita ba, sai dai a shekarun baya an rika wallafa wani sashensa ana bugawa a jaridar Attajdid. Sai littafin ‘Ahlul Baiti: Iyalan Babban Gida’ da littafin ‘Dujal Babbar Fitina’ da kuma littafin ‘Sallah Ginshikin Addini’ wanda shi ma Allah bai sanya ya fita ba. Haka kuma na rubuta littafin ‘Hajji: Ga Wanda Ya Sami Iko.’ Shi ma an yi amfani da shi shekaru masu yawa. A shekarar 2010 na fara fassarar Tafsirin Ibn Kasir, wanda zuwa yanzu aka samu nasarar kammalawa tare da fito da Juz’i na Farko da ke kunshe da izifi biyar (5) kuma yake dauke da kimanin shafi 500. Haka kuma na rubuta littafin ‘Tarihin Musulunci A Karni Na Ashirin (1900-2000).’
Haka kuma na rubuta mukala da yawa da aka gabatar a wasu tarurruka, wasu an buga su wasu kuma ba a buga su ba.
Kuma kamar yadda na fada a baya, kamfaninmu na wallafa AMBABA PRESS na yin ayyuka masu yawa na wallafa da gyara da fassara littattafai. A yanzu haka muna aikin tattara fassarar ‘Sahihul Bukhari’ na Jami’ar Bayero ta Kano, kuma muna aikin tattara Tafsirin Sheikh Dahiru Usman Bauchi zuwa littafi da sauran littattafai masu yawa.
Wadanne kalubale ka fuskanta, ko kake fuskanta a harkar rubuce-rubuce da wallafa?
Kalubalen bai wuce wanda kowane marubuci ko duk wani mai manufa a rayuwarsa yake fuskanta ba. Duk da haka ina godiya ga Allah bisa karamcinSa, domin rubuce-rubucen suna samun tagomashi a wurin al’umma, muna rokon Allah Ya karba mana. Kuma na samu tallafawar mutane masu yawa da ba zan manta gudunmawarsu game da wadannan rubuce-rubuce ba. A gaba-gaba, akwai marigayi Mai martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero (Allah Ya yi masa rahama), wanda shi ne ya fara daukar nauyin fara buga mana littafinmu na Tarihin Annabi Muhammadu (SAW) da Dokta Bashir Shehu Galadanci, wanda shi ya fara daukar nauyin buga littafinmu na Sahabbai (100), a lokacin yana Babban Mai Ba Gwamna Shawara a kan Ilimi da Sabuwar Fasahar Sadarwa a Jihar Kano da Injiniya Rabi’u Sulaiman Bichi da sauran mutane masu yawa, Allah Ya saka musu da alheri.
Idan ka kalli kanka a matsayin marubuci, yaya kake ji a ranka? Kana samun gamsuwa ko kana yin nadamar kasancewarka marubuci?
Ina ji a raina cewa, Allah Ya yi min babban karamci da Ya sanya ni a sahun marubuta na addinin Musulunci. Mutane da yawa ma suna alfahari da cewa sun san ni a matsayina na marubuci, don haka ban taba yin nadama ta kasancewa marubucin addinin Musulunci ba. Idan na waiga baya na ga yadda tafiyar take, ina kara gamsuwa da jin dadi da godiya ga Ubangijina, kuma ina fatan zai ci gaba da taimaka mana wajen wannan aiki.
Wane al’amari kake tunawa, kuma yake ba ka al’ajabi dangane da harkar rubuce-rubuce da wallafa?
Daga cikin abin da na fi tunawa a harkar rubutu shi ne farkon lokacin da aka buga littafinmu na ‘Tarihin Annabi Muhammad (SAW) Rahama Ga Talikai’ lokacin muna yara matasa kwarai da gaske, da yadda mutane da yawa suka rika yin fatan alheri da mamakin irin aikin da aka yi. Abu na biyu kuma shi ne lokacin da aka buga littafin tarihin Annabi (SAW) sai Malam Usman Musa Gabari ya kai wa wani mutuminsa, wanda babban jami’in gwamnati ne a lokacin. Da ya kai masa kwata-kwata bai dauki abin da muhimmanci ba, sai bayan shekaru ya sauka daga mukamin da yake kai, kwatsam wata rana sai ya dauko littafin ya duba shi. Abin ya ba shi mamaki cewa ashe littafin muhimmi ne. Nan da nan ya kirawo Malam Usman yana tambayar wai yaushe aka kawo masa littafin, kuma a lokacin me ya yi? Nan dai ya sanya shi a gaba kullum yana karantawa, kuma yana jinjina al’amarin, wannan ba na manta shi.
Ko kana da wani kira ko shawarwari ga marubuta irinka, da gwamnati da attajirai da sauran al’umma dangane da harkar littafi?
Shawarata ga marubuta, mu sake dagewa, tare da neman taimakon Allah. Ba wani abu mai muhimmanci da yake iya yiwuwa cikin sauki, sai an yi gwagwarmaya an dage sannan ake cin nasara. Haka kuma ina kira ga gwamnatocinmu da attajirai da sauran al’umma cewa su sanya hannunsu cikin wadannan ayyuka na alheri, aikin addinin Musulunci kama in kama ne, da haka sai ka ga an ci nasara baki daya.
Ko akwai wani bayani na kashin kanka da za ka yi wanda ban tambaye ka ba?
Ina fata da yardar Allah nan da wani lokaci in kammala fassarar Tafsirin Ibn Kasir. Ina kuma fatan al’ummarmu su ci gaba da amfana da dan wannan kokari, kuma ina rokon Allah Ya sanya musu albarka. Allah Ya karba mana.